Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai

Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai

- Dakarun sojoji sun ragargaji yan ta'adda a hanyar Abuja-Kaduna

- Lamarin wanda ya wakana a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, ya yi ajalin yan bindiga biyu

- Rundunar sojin ta kuma kwato wasu makamai daga hannun yan bindigan

Rundunar sojojin Najeriya a ci gaba da aikin kakkaba da take yi domin kawar da yan bindiga da sauran miyagu a fadin kasar, ta sake yin gagarumin nasara a kan yan bindiga.

Rundunar ta cimma wannan nasara ne a karkashin Operation Thunder Strike a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, a hanyar babbar titin Abuja-Kaduna.

An tattaro cewa an tura dakarun sojin ne zuwa yankin Rijana, bayan samun bayanai abun dogaro daga kwararru kan shige da ficen wasu yan bindiga a hanyar babbar titin Abuja zuwa Kaduna, hakan ya sa suka kai wa miyagun harin bazata.

KU KARANTA KUMA: Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai da harsasai
Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai da harsasai Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

Dakarun sojojin sun ragargaji yan ta’addan ta hanyar bude masu wuta, a cikin haka ne suka kashe mutum biyu yayinda sauran suka tsere da raunukan harbi.

Har ila yau a yayin arangaman, an samo bindigogi biyu, jagoran labarai na hedkwatar tsaro, John Enenche ne ya bayyana hakan.

A yanzu haka dakarun sojin na ci gaba da kasancewa a yankin inda suke sintiri domin hana su katabus a yankin.

KU KARANTA KUMA: An gano labarin matar da ta kashe ƴaƴanta 2 a Kano, da dalilin da ya sa ta kashe su

A wani labari na daban, 'Yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kai hari wasu yankuna biyu da ke karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Kamar yadda Katsina Post ta wallafa, yankunan da aka kai harin sune Tsauwa da Gandu.

Jaridar ta wallafa cewa, a kalla rayuka tara suka salwanta yayin da wasu da yawa suka samu miyagun raunika kuma aka yi garkuwa da wasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel