An Rantsar da Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, Manyan Jiga Jigai Sun Halarta
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Mutala Sule Garo a matsayin mataimkin gwamna a wani taro da aka shirya yau Talata, 5 ga watan Mayu, 2026
- Tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje da Malam Ibrahim Shekaru na cikin manyan bakin da suka halarci bikin rantsar da Garo
- Wannan na zuwa ne bayan Majalisar dokokin Kano karkashin jagorancin Rt. Hon. Jibril Isma'il Falgore ta tantance tare da amincewa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria – An rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano a wani taro da aka shirya a fadar gwamnati yau Talata, 5 ga watan Mayu, 2026.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigai da magoya bayan APC.

Source: Facebook
Babbar alkalin jihar Kano, Dije Aboki, ita ce ta rantsar da Murtala Garo, inda ta karanta masa rantsuwar kama aiki, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaoto.
Ganduje da manyan kusoshi sun halarta
Manyan jiga-jigan APC a Kano da mambobin Majalisar zartarwa sun samu halartar wannan gagarumin biki a fadar gwamnati yau Talata.
Daga cikin wadanda suka halarta akwai tsohon gwamnan Kano kuma tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau.
Haka zalika mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Falgore, da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II sun samu halartar wajen bikinn rantsuwar.
Jawabin da Murtala Sule Garo ya yi
Da yake jawabi bayan rantsar da shi, Murtala Garo ya nuna godiya ga gwamnan tare da yin alkawarin biyayya ga gwamnatin.
“Ina tsaye a nan cike da godiya da kuma nauyin alhakin da ke kaina a wannan muhimmiyar rana a rayuwata da kuma tafiyar wannan gwamnati.
“Na karbi wannan nauyi a matsayin kira na yi wa al’umma hidima tare da goyon bayan shugabancinka domin bunkasa jihar Kano.”
Ya kuma gode wa majalisar dokokin jihar bisa amincewa da nadinsa, yana mai cewa zai yi aiki tukuru domin nasarar manufofi da tsare-tsaren gwamnatin Abba.
“Ga al’ummar jihar Kano, ina mai tabbatar muku da cewa zan ci gaba da yi muku hidima. Wannan lokaci na bukatar hadin kai da ci gaba.
"Aikina shi ne tallafawa hangen nesa na wannan gwamnati tare da tabbatar da cewa manufofinta sun haifar da sakamako mai amfani,” in ji shi.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya ja hankalin Garo
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana nadin Garo a matsayin mataki na dabara domin karfafa hadin kai, tabbatar da nasarori da kuma samar da kwanciyar hankali.
“A wannan lokaci mai muhimmanci, jihar Kano na bukatar gogaggen shugabanci, hadin kai da kuma kwanciyar hankali na siyasa, yana da duka wadannan,” in ji Abba.
Ya kuma bukaci sabon mataimakin gwamnan da ya nuna cikakkiyar biyayya tare da aiki tare da gwamnati, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Ganduje ya kira Sanusi II da Sarki
An ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Ganduje ya kira Sanusi II da Sarki kuma Shugaban majalisar sarakunan Kano a yayin taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar, Murtala Sule Garo.
Mahalarta taron, sun kaure da tafi a lokacin da Ganduje ke gaishe da Sarki Sanusi II tare da kiran sa da "shugaban majalisar sarakunan jihar Kano".
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


