Sanata Kwari ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, ya jinjinawa Elrufai

Sanata Kwari ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, ya jinjinawa Elrufai

- Sanata Suleiman Abdu Kwari, ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli

- Kwari ya kuma jinjinawa Elrufai a kan zabin da yayi mai cike da hikima

- Sanatan ya kuma yi kira ga mutanen Zazzau da su ba sabon sarki hadin kai sannan su hada hannu wajen ci gaban masarautar

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta arewa, Suleiman Abdu Kwari, ya taya sabon sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murnar nada shi a matsayin sarki da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.

Yayinda yake jinjinawa karfin gwiwa da hikimar da ke tattare da zabar Bamalli da Gwamna Nasir El-Rufai yayi domin ya maye gurbin Marigayi Shehu Idris, sanatan ya yaba da hakuri da juriyar yan gidan sarautar Mallawa na fiye da shekaru 100.

KU KARANTA KUMA: Bayan nada shi sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya shiga fada

Da yake tuna cewa Malam Musa na gidan sarautar Mallawa ne kafa masarautar Fulanin Zazzau, Kwari ya ce gidan sun rasa sarautarsu tsawon shekaru sama da 100.

Sanata Kwari ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, ya jinjinawa Elrufai
Sanata Kwari ya yi mubaya'a ga sabon Sarkin Zazzau, ya jinjinawa Elrufai Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

“Lallai Gwamna El-Rufai ya yi aiki da hikima da karfin zuciya wajen tabbatar da cewar an zabi dan takarar da ya cancanta a sati biyu da aka yi ana takara.

KU KARANTA KUMA: Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

“Yayinda muke shiga sahun masu taya sabon sarki da gwamna murnar sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, muna kira ga yan uwanmu Zaga Zagi da su ba sabon sarki hadin kai sannan su hada hannu wajen ci gaban masarautar” in ji sanatan.

Sanata Kwari ya bayyana cewa shakka babu mutanen Zaria, cibiyar ilimi, sun yi imani da cewar mulki na Allah ne kuma Shi ke baiwa wanda Ya so.

A gee guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, murnar samun sarautar Zazzau.

Shugaban kasar ya kara da shawartarsa da ya zama shugaba ga kowa da kowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel