Wata Sabuwa: Trump Ya Hasala kan Iran, Ya Yi Babbar Barazana ga Kasar Musulunci
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ba da umarnin fara aikin 'Project Freedom' domin raka jiragen ruwa na kasuwanci su wuce ta mashigar Hormuz
- Donald Trump ya aika da sakon gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan yin katsalandan a sabon aikin da ya umarci a fara
- Shugaban na Amurka ya nuna cewa idan Iran ta farmaki jiragen ruwan da za su gudanar da aikin, za ta fuskanci gagarumar matsala
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin barazana ha Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya yi barazanar cewa za a ‘shafe Iran daga doron ƙasa’ idan ta yi katsalandan a mashigar ruwa ta Hormuz.

Source: Getty Images
Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne ga wakiliyar tashar Fox News a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.
Wace barazana Trump ya yi wa Iran?
Trump ya bayyana cewa za a “shafe Iran daga doron ƙasa” idan suka kai wa jiragen ruwan Amurka hari yayin da suke gudanar da aikin “Project Freedom” a mashigar ruwa ta Hormuz.
Shugaban na Amurka ya ce ya yi amanna Iran ta zama “mai sauƙin lallaɓawa” a tattaunawar zaman lafiya, sannan ya jaddada cewa ana ci gaba da ƙarfafa dakarun sojojin Amurka a yankin.
“Muna da makamai da alburusai masu ingancin da suka ninka waɗanda muke da su a baya."
“Muna da kayan aiki mafi kyau. Muna da kayayyaki a ko’ina a faɗin duniya. Muna da waɗannan sansanonin a ko’ina a faɗin duniya. Dukkaninsu shake suke da kayan aiki. Za mu iya amfani da dukkan waɗannan kayayyakin, kuma za mu yi hakan idan bukatar hakan ta taso.”
- Donald Trump
An ja kunnen Iran kan taba kadarorin Amurka
Hakazalika, kwamandan rundunar CENTCOM na Amurka, Admiral Brad Ccoper, ya shawarci Iran da ta nesanci kadarorin Amurka.

Kara karanta wannan
Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka
Admiral Brad Cooper ya ce dakarun Amurka sun nutsar da jiragen ruwan Iran guda shida da suka yi ƙoƙarin tsoma baki a harkar sufurin jiragen kasuwanci a mashigar Hormuz, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.

Source: Twitter
Kwamandan ya kuma dakarun sun kakkabo makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi na Iran a yayin aikin “Project Freedom” don buɗe mashigar Hormuz.
Admiral Brad Cooper ya ce ya ba wa dakarun Iran shawara da su nesanci kadarorin sojin Amurka yayin gudanar da aikin, sannan ya jaddada cewa Amurka na ci gaba da killace tashoshin jiragen ruwa na Iran, aikin da ya ce yana “tafiya fiye da yadda ake tsammani”.
Iran ta ja kunnen shugaban Amurka, Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aika da sakon gargadi ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump, kan shirin rakiyar jiragen ruwa da suka makale a mashigar Hormuz.
Shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin Iran, Ebrahim Azizi, ya gargadi Amurka kan tsoma baki a mashigar Hormuz.
Ya bayyana cewa cewa duk wani katsalandan da Amurka za ta yi a tsarin zirga-zirgar ruwa a mashigar Hormuz za a dauke shi a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Asali: Legit.ng
