Shekarau Ya Fara Samun Matsala bayan Dawowa APC, an Taso Shi a Gaba kan Takara

Shekarau Ya Fara Samun Matsala bayan Dawowa APC, an Taso Shi a Gaba kan Takara

  • Matasan ƙungiyoyin ɗalibai a Kano sun ƙi yunƙurin maye gurbin ɗan takarar da suke so da Malam Ibrahim Shekarau
  • Ana zargin za a maye gurbin Abdulsalam Abdulkarim Zaura da Malam Ibrahim Shekarau a takarar Sanatan Kano ta Tsakiya
  • Ƙungiyoyin sun bayyana cewa biyayya da sadaukarwar Zaura ga APC sun cancanci ba shi takara, suna gargadin cewa sauya shi zai haifar da rashin adalci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya koma jam’iyyar APC mai mulki bayan ya shafe lokaci a jam’iyyar adawa.

Ƙungiyoyin ɗalibai a Kano sun nuna adawa da jita-jitar da ke cewa ana shirin maye gurbin Abdulsalam Abdulkarim Zaura da Shekarau a takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

An taso Shekarau a gaba kan takarar sanata
Malam Ibrahim Shekarau da Abdulsalam Abdulkarim Zaura. Hoto: Malam Ibrahim Shekarau, A A Zaura.
Source: Facebook

An ƙi amincewa da shirin ba Shekarau takara

Kara karanta wannan

Oshiomhole ya nemi Tinubu ya soke lasisin MTN da wasu kamfanonin Afrika ta Kudu

Ƙungiyoyin sun haɗa da Concern Kano Citizens, NANS Kano Axis, NAKSS da kuma haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ɗaliban Arewa, cewar The Guardian.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano ranar Litinin, jagoran ƙungiyar Inyass Muhammad Auwal ya ce sun damu da abubuwan da ke faruwa a APC.

Auwal ya bayyana cewa wasu mambobin APC na yaɗa bayanan da ke nuna ana son bai wa Shekarau tikitin takarar sanata maimakon Zaura.

Ya ce duk da babu wata sanarwa daga gwamnati ko shugabannin APC, suna kira ga jam’iyyar ta dakatar da duk wani yunƙuri mara kyau.

A cewarsa, suna girmama Shekarau a matsayin dattijo kuma uba, amma adalci yana buƙatar a saka wa masu biyayya da sadaukarwa.

Matasa sun ki amincewa da shirin kakaba masu Shekarau a matsayin ɗan takara
Dan jam'iyyar APC a Kano, Abdulsalam Abdulkarim Zaura. Hoto: AA Zaura Media.
Source: Twitter

Ana zargin 'shirin' za a ci amanar Zaura

Auwal ya ce bayan Murtala Sule Garo ya samu matsayi a ɓangaren zartarwa, ya dace a bai wa AA Zaura damar sake tsayawa takara.

Ya gargadi APC cewa cire Zaura domin bai wa wani sabon dawowa tikiti zai nuna jam’iyyar ba ta daraja jajircewa da biyayya, cewar PM News.

Kara karanta wannan

An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi

Jagoran ya ce har yanzu ba su ji wata sanarwa daga gwamna ko shugabannin APC ba, kuma suna fatan jita-jitar ba gaskiya ba ce.

Ya kuma roƙi magoya bayan Zaura su kwantar da hankalinsu tare da guje wa duk wani mataki da zai haddasa tashin hankali a Kano.

A ƙarshe, Auwal ya roƙi Ibrahim Shekarau da kada ya bari a yi amfani da sunansa wajen haddasa rashin adalci ga waɗanda suka tsaya wa APC.

Sauya sheka: Zaura ya ƙare APC

Mun ba ku labarin cewa jagora a jam'iyyar APC mai mulki, AA Zaura ya yi magana kan zargin cewa ana bai wa mutane kuɗi domin su sauya sheka.

Dan siyasar ya ce sauya sheƙar da ake yi daga jam’iyyu zuwa APC ya samo asali ne daga amincewa da shugabancin Bola Tinubu da salon mulkinsa.

AA Zaura ya yi magana ne yayin da aka yawaita cewa jam'iyya mai mulki na sayen 'yan adawa da makudan kudi zuwa APC inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne ko kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.