Kotu ta yi watsi da bukatar Zakzaky, ta umarci a ci gaba da shari’arsa

Kotu ta yi watsi da bukatar Zakzaky, ta umarci a ci gaba da shari’arsa

- Wata babbar kotu a Kaduna ta umarci a ci gaba da shari’ar da aka kawo gabanta kan shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky

- Kotun ta yi watsi da bukatar Zakzaky da matarsa Zeenat na neman a soke tuhume-tuhumen da gwamnatin Kaduna ke yi masu

- Akalin kotun ya ce hakan ba mai yiwuwa ba ne domin bai gama sauraron gundarin karar da aka shigar ba balantana ya yanke hukunci

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta yi watsi da takardar da shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria(IMN), Sheikh Ibrahim El-Zazaky da matarsa Zeenat suka cike na neman a kori shari’arsu.

Dukkaninsu su biyu suna fuskantar shari’a a kan tuhume-tuhume takwas da ake masu na taro da baya bisa ka’ida, haddasa rashin zaman lafiya a cikin jama’a da dai sauransu.

Shugaban kungiyar na Shi’a, wanda aka gurfanar a gaban kotu a safiyar yau Talata, cikin tsautsaran tsaro, ya bukaci kotu da ta soke shari’ar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar a kansu saboda rashin hujja.

KU KARANTA KUMA: A ƙarshe: Gwamna Zulum ya magantu kan harin da Boko Haram ta kai masa har sau biyu

Kotu ta yi watsi da bukatar Zakzaky, ta umarci a ci gaba da shari’arsa
Kotu ta yi watsi da bukatar Zakzaky, ta umarci a ci gaba da shari’arsa Hoto: @Sh4Zk
Asali: Twitter

A yayin zama na karshe da aka yi a ranar 7 ga watan Agusta, alkalin da ke jagorantar shari’an, Justis Gideon Kurada, ya saka ranar yau domin yanke hukunci.

Hakan ya biyo bayan lauyoyin wadanda ake kara, Abubakar Marshall da Femi Falana, sun bukaci kotu da ta soke tuhume-tuhumen da gwamnatin ke yiwa su Zakzaky.

Sun bukaci hakan ne kan “rashin bayyana wani laifi da doka ta sani wanda ya kara da sashi na 36 (8) da (12) na kundin tsarin mulki na 1999.

Lauya mai gabatar da kara, Dari Bayero, shima ya gabatar da sharhinsa na karshe kan lamarin.

Justis Gideon Kudafa, ya yi watsi da bukatar a kori shari’ar da aka gabatar masa, cewa hakan ba mai yiwuwa ba ne saboda bai gama sauraron gundarin karar da aka shigar ba.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Majalisar Dattijai ta dawo bakin aiki bayan hutun makonni takwas

Sai dai, Elzakzaky da matarsa sun musanta zarge-zargen da ake musu, bayan an karato masu su, Channels TV ta ruwaito.

Alkalin dai ya tsayar da Nuwamba a matsain watan ci gaba da sauraron karar.

An dage shari’an zuwa ranakun 18 da 19 ga watan Nuwamba, 2020 domin ci gaba da sauraronsa da kuma ba lauyan mai kara damar gabatar da shaidarsa a gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel