Sabon Sarkin Zazzau: An sanya sunan Bamalli a masu takara

Sabon Sarkin Zazzau: An sanya sunan Bamalli a masu takara

- Alamu sun nuna gwamnatin jihar Kaduna ta sauya takardar da ke dauke da jerin sunayen mutane uku da ake ganin sune manyan yan takarar kujerar sarkin Zazzau

- An tattaro cewa an saka sunan na hannun daman Gwamna Nasir El- Rufai, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli cikin yan takarar, yanzu sun zama hudu kenan

- Sunan Bamalli dai baya cikin jerin sunayen mutanen da majalisar nadin sarki ta mika da farko

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sauya takardar da ke dauke da jerin sunayen mutane uku da ake ganin sune manyan yan takarar kujerar sarkin Zazzau da majalisar masu nadin sarki suka gabatar.

An gabatarwa da gwamnati sabon takarda da ke dauke da sunayen mutane hudu, ciki harda na hannun daman Gwamna Nasir El- Rufai, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, wanda babu sunansa a na farko a ranar Lahadi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Bamalli ne Magajin Garin Zazzau.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi

Sabon Sarkin Zazzau: An sanya sunan Bamalli a masu takara
Sabon Sarkin Zazzau: An sanya sunan Bamalli a masu takara Hoto: The Big Chill Read
Source: UGC

Kwanaki bakwai kenan da rasuwar Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu yana da shekaru 84 bayan yar gajeriyar rashin lafiya a asibitin sojoji da ke Kaduna.

Sai dai kuma har yanzu ba a san wanda zai zama sarkin Zazzau na 18 ba.

An tattaro cewa mutane na cike da zullumi a Zaria yayinda mazauna yankin ke ta baza kunnuwa don jin sanarwar wanda zai zama sabon sarkinsu.

KU KARANTA KUMA: Sabon sarkin Zazzau: Na shiga littafi na uku kuma na karshe, inji El-Rufai

A gefe guda, mun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ba za ta yi amfani da rahoton da majalisar nadin sarki na masarautar Zazzau ta kai mata ba domin cike gurbin sarkin.

Wannan hukuncin ya dawo da Ahmed Bamalli, wanda aka tabbatar da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ke so a cikin masu zawarcin karagar mulkin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel