Tinubu Ya Yi Martani da Murtala Garo Ya Zama Sabon Mataimakin Gwamnan Kano

Tinubu Ya Yi Martani da Murtala Garo Ya Zama Sabon Mataimakin Gwamnan Kano

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Murtala Sule Garo murna bayan rantsar da shi a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Kano
  • Gwamna Abba Yusuf ne ya naɗa Garo domin cike gurbin da Aminu Abdulsalam ya bari bayan ya yi murabus sakamakon sauya sheƙar gwamnan
  • Shugaba Tinubu ya bayyana yadda wannan naɗi zai ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar APC a jihar Kano yayin da ake tunkarar zabukan 2027

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga Alhaji Murtala Sule Garo biyo bayan rantsar da shi da aka yi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano.

Legit Hausa ta rahoto cewa, an rantsar da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano na biyu a ƙarƙashin gwamnati mai ci ne a ranar Talata, 5 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

A karon farko, Ganduje ya amince da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano

Tinubu ya taya Murtala Garo murnar zama mataimakin gwamnan Kano
Murtala Sule Garo (dama) ya na karanta rantsuwar zama mataimakin gwamnan Kano. Hoto: King EL Dawud
Source: Facebook

Tinubu ya taya Murtala Garko murna

Sakon taya murnar Tinubu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar, wadda Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X.

Yayin da Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan wannan zaɓi da ya yi na daukar Murtala Garo a matsayin mataimakinsa.

Sanarwar Onanuga ta ce:

"Shugaba Bola Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo, sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, biyo bayan rantsar da shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar Talata.
"Gwamna Yusuf ya nada Garo ne domin ya maye gurbin kujerar da Aminu Abdulsalam ya bari, sakamakon sauya shekar da gwamnan ya yi zuwa jam'iyyar APC."

Kadan daga tarihin ayyukan Murtala Garo

Murtala Sule Garo, mai shekaru 48, ba baƙon fuska ba ne a fagen siyasar jihar Kano, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a baya, kamar yadda sanarwar Onanuga ta nuna.

Kara karanta wannan

NDC ta buɗewa Obi ƙofa, ta mika tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudancin Najeriya

Sanarwar ta nuna cewa Garo ya taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Kabo, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi da al’amuran masarautu a zamanin gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, sabon mataimakin gwamnan ne ya kasance abokin takarar Nasir Yusuf Gawuna, d'an takarar gwamna na jam'iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2023.

An kammala rantsar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.
Abdulaziz Abdulaziz, Murtala Garo, Gwamna Abba Yusuf sun yi hoto da wasu kusoshin APC bayan rantsar da mataimakin gwamna. Hoto: King EL Dawud
Source: Facebook

Karfafa hadin kan jam'iyyar APC

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa wannan naɗi zai taimaka ƙwarai wajen samar da haɗin kan da ake buƙata a cikin jam'iyyar APC a jihar Kano.

Shugaban ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a jihar da su mara wa gwamnan da mataimakinsa baya domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci.

A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Murtala Garo fatan alheri a sabon nauyin da aka ɗora masa, tare da ƙarfafa shi kan ya yi aiki kafa-da-kafa da gwamna domin amfanin al'ummar jihar Kano.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Maganar Ganduje a taron rantsar da Garo

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wata magana a taron rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar da ta ja hankali.

Kara karanta wannan

Yunwa a Arewa: Tinubu ya ware tireloli 100 na abinci, makudan kudi ga jihohi 19

A taron rantsuwar da aka yi ranar Talata, Ganduje ya kira Muhammadu Sanusi II a matsayin 'Sarkin Kano' kuma 'shugaban majalisar sarakunan jihar.'

Wannan ne karon farko da aka ji Ganduje, tsohon shugaban jam'iyyar APC ya amince da Sanusi II a matsayin sarkin Kano tun bayan tsige shi da ya yi a lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com