Yunwa a Arewa: Tinubu Ya Ware Tireloli 100 na Abinci, Makudan Kudi ga Jihohi 19
- Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya karɓi bakuncin uwargidan shugaban ƙasa a Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu a jihar
- Uba Sani ya hadu da Oluremi ne domin ƙaddamar da rabon motocin shinkafa 100 da tallafin Naira biliyan 1.2 a Arewacin Najeriya
- Uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ce shirin tallafin zai taimaka wajen rage wahalar rayuwa ga gidaje masu ƙaramin ƙarfi a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamna Uba Sani ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan jagoranci da manufofin da yake aiwatarwa domin farfaɗo da tattalin arziki da haɗin kan ƙasa
Gwamnan ya tarbi uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, domin ƙaddamar da rabon tallafin a gidajen marasa ƙarfi da masu bukata a Arewa.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da Gwamna Uba Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya 30 ga watan Afrilun shekarar 2026 da muke ciki.
Bola Tinubu ya ware wa jihohin Arewa tallafi
Tallafin ya haɗa da motocin shinkafa guda 100 da kuma kuɗi har Naira biliyan 1.2 da za a rabawa jihohin Arewa 19 da Abuja.
Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na nuna tausayi da kulawa ga talakawa, yana mai cewa ba kawai bikin ƙaddamarwa aka yi ba.
Ya ce ya yi amfani da damar wajen gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jagoranci mai cike da hangen nesa da yake bayarwa a ƙasar nan.
Uba Sani ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu na “Renewed Hope” suna taimakawa wajen dawo da ƙwarin gwiwa da inganta rayuwar jama’a a Najeriya.
Ya yabawa uwargidan shugaban ƙasa bisa jajircewarta wajen aiwatar da shirye-shiryen da ke tallafawa marasa galihu ba tare da nuna bambanci ba.

Source: Facebook
Yabon da Oluremi ta samu daga Uba Sani
Gwamnan ya ce ayyukan Remi Tinubu suna taɓa rayuwar jama’a kai tsaye tare da dawo da martaba da bege tsakanin mabambantan addinai da ƙabilu.
Ya kuma yabawa haɗin gwiwar da aka samu tsakanin kungiyar 'Muslim Intellectuals Forum' da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa.
Gwamnan ya ce kiran Kaduna a matsayin zuciyar Arewa babban abin alfahari ne da ke ƙara musu ƙwarin guiwar ci gaba da aiki domin haɗin kai da cigaba.
Uba Sani ya gode wa shugabannin addinai saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da kyawawan ɗabi’u a Kaduna.
Tudun Biri: Gwamnonin Arewa sun tallafa wa Musulmi
A baya, an ji cewa gwamnonin jihohi 19 na Arewa sun haɗa gudummuwar N180m sun baiwa mutanen da harin sojoji ya shafa a Tudun Biri.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ne ya faɗi haka bayan kammala taron da suka yi a Kaduna.
Inuwa ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu tare da kira ga gwamnatin tarayya ta biya diyya domin kare faruwar haka a nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

