Tashin Hankali: An Bindige Mahaifin Amarya Ana tsaka da Bikin Auren ’Yarsa
- An shiga tashin hankali yayin bikin aure inda mahaifin amarya ya bakunci lahira ana tsaka da cashewa bayan harin yan daba
- Ana zargin ’yan daba ne suka harbe mahaifin amaryar da wani mai nishaɗantarwa mai suna Victor har lahira a wani bikin a Ikotun a Lagos
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa wajen liyafar ana biki tare da bude wuta, lamarin da ya haddasa firgici da gudun ceton rai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikotun, Lagos - An shiga ruɗani a yankin Ikotun da ke Lagos bayan wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kashe mahaifin amarya.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa bayan kashe mahaifin amaryar, an kuma bindige wani mai nishaɗantar da jama'a mai suna Victor.

Source: Twitter
An kashe mahaifin amarya a bikin auren 'yarsa
Lamarin ya faru ne a titin Oviawe da ke kusa da hanyar 'Governor' bayan kammala bikin aure inda baƙi suka taru domin gudanar da liyafar bayan biki, cewar Punch.
Wani mazaunin yankin mai suna Tosin ya bayyana cewa Victor na tsakiyar nishaɗantar da baƙi lokacin da maharan suka shigo tare da fara harbe-harbe.
Ya ce jama’an da ke wurin sun rika gudu domin ceton rayukansu yayin da maharan suka jawo Victor zuwa bakin titi suna dukansa da muggan makamai.
Yadda mahara suka kashe mahaifin amarya
Wani mazaunin yankin ya ce mahaifin amaryar ya yi ƙoƙarin shiga tsakani domin ceto Victor, amma maharan suka harbe su biyun nan take.
Majiyar ta ce mutanen biyu sun mutu a wurin, lamarin da ya jefa mazauna yankin da masu sana’o’i cikin tsananin fargaba da rudani.
Rahotanni sun nuna cewa harin na iya kasancewa yana da alaƙa da rikicin ’yan daba da ake fama da shi a yankin na Ikotun.

Source: Original
Mutane sun yi magana kan marigayi Victor
Wani mazaunin yankin mai suna Steve ya ce Victor sanannen mutum ne a unguwar kuma ana yawan ganinsa yana gudanar da harkokinsa cikin lumana.
Har ila yau, wani mazaunin yankin ya ce abin da ya faru ya tayar masu da hankali inda ya roki hukumomi su dauki matakin da ya ce, cewar Daily Post.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a gano sunan mahaifin amaryar ko kuma waɗanda suka kai harin ba a hukumance.
Kakakin rundunar ’yan sandan Lagos ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa za a tura binciken zuwa sashen SCID da ke Panti domin ci gaba da bincike.
An bindige ango ranar aurensa a Delta
A baya, mun ba ku labarin cewa kisan gilla da aka yi wa wani ango a yankin Kwale a karamar hukumar Ndokwa a Delta ya jefa al'umma a tashin hankali.
Wasu miyagu dauke da bindiga sun kai farmaki kan mutane, suka kashe wani ango a ranar Juma'a ana tsaka da shirin daurin aurensa.
Shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa an kashe angon ne yayin da yake tafiya sayayya tare da wasu abokansa a safiyar ranar Juma'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

