Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa

- Wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa kwararrun ma su kisa ne sun harbe dagachin kauyen Runji, Alhaji Musa Abubakar

- 'Yan bindigar sun yi watsi da tayin kudi da na mota da marigayin ya yi niyyar ba su domin su barshi da ransa

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton an dauko hayarsu don aikata kisa sun kashe Alhaji Musa Abubakar, Dagachin kauyen Runji da ke mazabar Auchan a karamar hukumar Ikara, jihar Kaduna.

'Yan ta'addar sun kashe Basaraken ne da duku-dukun safiyar ranar Lahadi bayan sun kutsa kai zuwa cikin gidansa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Suleiman Musa, da wurin marigayin, ya sanar da ita cewa 'yan bindigar sun harbi mahaifinsa har sau hudu.

Suleiman, wanda shi ma dagachi ne a kauyen Rafin Rogo, ya sanar da Daily Trust cewa; "wasu 'yan bindiga sun shiga gidan Sarki da misalin karfe 2:00 na safiyar ranar Lahadi. Sun shiga gidan cikin sauki sun yi ma sa kilan gilla.

KARANTA: 'Yan bindiga sun harbe dan majalisa yayin da ya ziyarci mazabarsa domin halartar taron siyasa

"Sun tsallaka katangar gidan, ta haka su ka samu damar shiga. Sun fito da shi tsakar gida tare harbinsa sau hudu.

"Sun zo ne don su hallaka shi kawai, ba don su karbi wani abu a hannunsa, saboda har tayin zai basu kudi ya yi mu su, amma su ka ki karba, ya basu motarsa, su ka ce ba za su karba ba domin an aikosu ne kawai su kashe shi," a cewar Suleiman.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa
Gwamnan jihar Kaduna; Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

Kazalika, shugaban karamar hukumar Ikara, Salisu Ibrahim, ya tabbatarwa da Daily Trust cewa 'yan bindiga sun kashe dagachin kauyen Runji har gida ranar Lahadi.

KARANTA: Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makaman kungiyar Boko Haram/ISWAB daga ketare

Salisu ya bayyana cewa karamar hukuma ta tura karin jami'an tsaro zuwa yankin da abin ya faru domin tabbatar da cewa an kama 'yan ta'addar da su ka kashe marigayi Alhaji Musa.

Sannan, ya roki jama'a su bawa jami'an tsaro hadin kai tare da ba su muhimman bayanai a kan harkokin duk wasu 'yan ta'adda da sauran ma su aikata miyagun laifuka.

An yi jana'izar marigayi Alhaji Musa, bisa tsarfin addinin Musulunci, da safiyar ranar Lahadi bisa tsarin addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng