Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau

Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya soke zaben farko da masu zaben sarkin Zazzau suka yi

- A yanzu haka masu zaben na gudanar da sabon nazari kan dukkanin yan takara 13 da suka nuna ra'ayin son zama Sarkin Zazzau na gaba

- Hakazalika an mayar da yan takara biyu da aka cire a baya

Tsarin zaben Sarkin Zazzau na 19 ya dauki sabon salo a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba.

A yanzu haka masu zaben Sarki a masarautar Zazzau na kan sabon matakin zabe, kamar yadda babban sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya bayyana.

Balarabe ya yi bayanin cewa gwamnan ya yi umurnin sake sabon zagaye na zabe bayan ya soke na farkon da aka yi, inda aka cire yan takara biyu.

Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau
Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

Gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na twitter cewa: “A yanzu haka masu zaben sarki sun hadu don sake sabon nazari kan dukkanin yan takara 13 da suka nuna ra’ayinsu kan kujerar daga dukkanin gidajen sarauta, ciki harda mutane biyu da aka cire a baya. Za' a gabatar da rahoton nasu ga gwamna domin dubawa.

“A yanzu haka, masu zaben sarki na masarautar Zazzau na gudanar da sabon nazari don zabo wanda za a nada cikin masu takarar da zai zama Sarkin Masarautar Fulani ta Zazzau na 19.

''Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin yin sabon zagaye na zaben bayan da ta soke na farko da aka fara, inda aka cire yan takara biyu."

KU KARANTA KUMA: Sabon rahoto: Ministan ƙwadago ya faɗi lokacin da ASUU za ta janye yajin aikin da ta shiga

Muyiwa Adeleye, mai ba Gwamnan jihar shawara a kafofin watsa labarai, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa daya daga cikin yan takarar, Bunu Zazzau ya yi korafin cewa bai samu damar gabatar da takardar takararsa ba: “saboda an fada masa cewa an rufe karba.

“Hakazalika, Sarkin Dajin Zazzau ma ya yi zanga-zanga a kan cire shi da aka yi daga tsarin. An kuma lura cewa masu zaben Sarkin sun tantance yan takara biyu a ranar 24 ga watan Satumba, 2020, ba tare da sun ga takardunsu ba wanda aka karba a washegari.”

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Ƴan ta'adda sun kashe sojojin Nigeriya 10 a harin kwantan ɓauna

A gefe guda, Babban malamin addinin nan, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana game da yadda ake zaben shugabanni idan ana da masu neman takara.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana hanya mai sauki da za a zabi shugaba wanda zai samu goyon bayan duk sauran abokan takararsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel