Sulaiman Dabo ya ce Gwamnan Kaduna bai kawo kudirin raba Masarauta ba

Sulaiman Dabo ya ce Gwamnan Kaduna bai kawo kudirin raba Masarauta ba

- Ana rade-radin cewa za a barka Masarautar Zazzau zuwa kasashe uku

- ‘Dan Majalisar Zariya, Hon. Sulaiman Dabo ya karyata wannan jita-jita

- Dabo ya ce gwamnan Kaduna bai kawowa majalisa wannan kudirin ba

Rade-radi sun yadu cewa akwai yunkurin rarraba masautar Zazzau zuwa kasashe uku, inda za a nada sababbin sarakuna a Kudan, Kaduna da Zariya.

‘Dan majalisar da ke wakiltar Zariya, Honarabul Sulaiman Ibrahim Dabo, ya yi maza ya yi magana game da wannan batu domin fitar da jama’a daga duhu.

Sulaiman Ibrahim Dabo ya ce a matsayinsa na ‘dan majalisar dokokin jihar Kaduna, sam babu gaskiya a jita-jitar da aka fara yadawa a makon nan.

KU KARANTA: Bamalli ya shiga cikin sunayen masu neman takara a Zazzau

Sulaiman Dabo wanda ya ke rike da kujerar Wakilin Birnin Zazzau ya ce gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai bai kawo masu wannan kudiri ba.

‘Dan majalisar ya tabbatar da cewa a zaman da su ka yi na ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, sun tattauna ne game da kasafin kudin shekara mai zuwa.

Hon. Dabo ya yi kira ga masu yada wannan jjita-jita da su daina wannan danyen aiki, su koma yi wa kasar Zazzau addu’ar samun sabon Sarki mai adalci.

Legit.ng ta samu labari cewa Wakilin Birnin Zazzau ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Facebook, jim kadan bayan sun fito daga zaman majalisa.

Sulaiman Dabo ya ce Gwamnan Kaduna bai kawo kudirin raba Masarauta ba
Sulaiman Dabo Wakili Hoto: Twitter/Bashir Dabo
Asali: Twitter

KU KARANTA: An yi shekaru 2 babu Sarki a Jihar Kaduna

Ya ce: “A matsayina na Danmajalisa mai wakiltar mutanen Zaria birni kuma Wakilin Birnin Zazzau, Ina ta ganin ana ta yada jita-jita cewa Mai girma Gwamnan Kaduna ya kawo kudiri don a raba masarautan Zazzau gida uku.”

“Wannan magana ba gaskiya bane. Yanzu muka fito daga majalisa amma Gwamna ya kawo mana Kasafin kudin 2021.”

A karshe ya rubuta: “Don haka don Allah a Kula da yada jita-jita. Allah ya zaban mana Adalin Sarki alfarman Manzon tsira (SAW).”

Yanzu nan kuma mu ka ji cewa Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu. Marigayin ya fito ne daga gidan Sarki Bayero.

Za ayi jana’izarsa da karfe 2:00 na rana a Kofar Kudu da ke Masarautar Kano a cikin Birni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel