PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki

PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki

- Wasu mahara sun kai wa mamba mai wakiltan mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, da wasu mutane da ke cikin motarsa hari

- Sai dai babu wanda ya ji rauni a cikinsu amma yan bindigan sun yi kaca-kaca da motar

- Jam'iyyar PDP ta yi martani kan haka, ta bukaci gwamnatin jihar ta inganta tsaro a fadin Kaduna

Yan bindiga sun kai wa mamba mai wakiltan mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, da wasu mutane da ke cikin motarsa hari a ranar Asabar, a hanyar Kwoi-Fadan Kagoma da ke karamar hukumar Jaba a jihar Kaduna.

An tattaro cewa dan majalisar da sauran mutanen da ke motar sun kubuta ba tare da rauni ba, amma dai motarsu ta yi kaca-kaca sakamakon harbe-harben yan bindigan.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga sakataren labarai na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, Abraham Alberah Catoh, a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

A kan haka, jam’iyyar PDP ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tsaurara matakan tsaro a yankin da ma fadin jihar gaba daya, jaridar Sun ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki
PDP ta yi kira ga inganta tsaro a Kaduna: Yan bindiga sun kai wa dan majalisar wakilai farmaki Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

“An janyo hankalin jam’iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) reshen jihar Kaduna zuwa ga harin da aka kai wa dan majalisar wakilai, mai wakilan mazabar Jema’a/Sanga, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, a hanyar Kwoi-Fadan Kagoma, a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba, 2020.

“An gode Allah babu abunda ya samu dan majalisar da mutanen da ke cikin motar, amma dai motar ya yi kaca-kaca da harbin bindiga.

“Mummunan al’amarin ya afku ne a yankin da ba a samu matsalar rashin tsaro ba na tsawon lokaci. Abun bakin ciki ne cewa wannan hari shine na farko da aka fara samu.

“Jam’iyyar bata ji dadin haka ba cewa hukumomin tsaro basa sauke hakkin da ya rataya a wuyansu. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi a kan ayyukansu sannan su bi sahun miyagun domin hana afkuwar hakan a gaba.

“Mu na kira ga gwamnati da ta inganta hakkin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, wanda ta gaza sosai wajen saukewa.

“Garkuwa, hare-haren ta’addanci da fashi da makami na wakana a fadin jihar.

“PDP ta shiga dimuwa sannan ta yi al’ajabin cewa idan har rayuwar wanda ke wakiltan mutane a majalisar dokokin tarayya na cikin barazana, toh ya rayuwar talaka za ta kasance?

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

“Jam’iyyar ta yi kira ga mazauna yankin kan su kwantar da hankalinsu, sannan ta shawarce su da su zama masu bin doka da taimakawa hukumomin tsaro da bayanai masu amfani domin kakkabe ayyukan miyagu a yankin da sauran yankunan Kaduna.”

A wani labari na daban, shugaban IAZE, Sheikh A. G Mika'il ya sanar da manema labarai a birnin Kebbi yadda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da mutane 18 a jihar Kebbi.

Ya roki jami'an tsaro da su taimaka su cetosu daga hannun 'yan bindigan.

A ranar 25 ga watan Satumbar 2020, 'yan bindiga sun kai hari, inda suka kashe mutum 1 a Akawo, suka kuma kashe mutane 2 a 'Yar Kasuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng