Yaki da ta'addanci a Najeriya
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa dan ta'adda, Bello Turji bai gagari hukuma ba kuma da yarfae Alah ya kusa shiga hannun jami'an tsaron Najeriya.
Yan majalisar wakilan tarayya na jam'iyyun adawa sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci kasar nan yadda ya kamata ko ya yi murabus.
Shugabannin Musulmi da na Katolika a Najeriya sun bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa domin kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane.
Wasu mambobin Majalisar Wakilai sun zargi gwamnatin Bola Tinubu da fifita siyasar zaɓen 2027 kan magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da dimokuraɗiyya.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta tattauna da duk wani dan ta'adda da ya amince zai daina aikata miyagun laifuffuka.
Yayin da rashin tsaro ya yi ƙamari a Katsina, Yan sanda sun umarci rundunar a jihar ta ƙara tsaurara matakan tsaro a makarantu domin kare ɗalibai.
Babbar kotun tarayya da ke Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa bayan samun ta da laifin taimaka wa ‘yan bindiga ta hanyar kai masu harsasai.
Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta fara shari'a a zagayen na biyu kan fiye da mutum 600 da ake zargi da ta’addanci a kotunan birnin tarayya da ke Abuja.
Akalla 'yan sanda uku aka tabbatar da sun rasa rayukansu yayin da motar sulke ta taka bam da ake zargin yan ta'adda ne suka dasa a jihar Zamfara.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari