Kotu Ta Yanke wa Wasu Ƴan Ta'adda Hukuncin Kisa bayan Amsa Laifuffukansu
- Wata babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya a birnin Abuja
- Danladi Lawal, Abdullahi Mohammed da Mohammed Gulama Shaibu sun amsa laifuffukan da ake zarginsu da su
- Alkalai sun kuma yanke hukuncin daurin rai da rai da shekaru masu yawa ga wasu da aka samu da laifuffukan goyon bayan ta’addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya a birnin tarayya.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta same su da laifuffukan ta’addanci a ranar Alhamis 18 ga watan Yunin 2026.

Source: Facebook
An yanke musu hukuncin ne bayan sun amsa laifuffukan da Gwamnatin tarayya ta tuhume su da su a ci gaba da shari’o’in ta’addanci da ake yi a kotun, cewar Punch.
Yan ta'addan sun amsa laifuffukansu a kotu
Mai shari’a James Omotosho ya yanke wa Danladi Lawal hukuncin kisa, yayin da Mai shari’a Salim Ibrahim ya yanke irin wannan hukunci ga Abdullahi Mohammed da Mohammed Gulama Shaibu.
Lokacin da aka kira shari’ar Lawal, wanda aka fi sani da Dankawu kuma mai shekaru 33, ya amsa laifuffuka biyar da aka karanta masa.
Bayan amsa laifuffukan, kotu ta yanke masa daurin shekaru 30 a laifi na farko, shekaru 15 a na biyu, daurin rai da rai a na uku.
Sannan kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a laifi na hudu, tare da daurin rai da rai a laifi na biyar.
Mai shari’a Omotosho ya ce wa wanda aka yankewa hukuncin alkalin ya ce:
“Allah Ya ji kanku da rahama.”

Source: Getty Images
Laifuffukan da yan ta'addan suka aikata
A cikin takardar tuhuma mai lamba FHC/KNJ/CR/956/2026, Gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ta gurfanar da Lawal kan tuhume-tuhume biyar.

Kara karanta wannan
Kotu ta yi hukunci za a rataye jagoran dabar yan bindiga Jibrin Halilu har lahira
A laifi na hudu da ya jawo hukuncin kisa, an ce Lawal tare da wasu da har yanzu ba a kama ba sun aikata laifin a shekarar 2020.
An ce sun yi garkuwa da wani dattijo tare da tsare shi tsawon kwanaki hudu a wani daji da ke Ilela, cewar Tribune.
Bayan haka sun nemi kudin fansa N950,000 daga iyalansa, abin da ya haifar da tsoro da rashin tsaro a yankin.
Hakazalika, Mai shari’a Salim Ibrahim ya yanke wa Abdullahi Mohammed da Mohammed Gulama Shaibu hukuncin kisa bayan sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.
Mohammed ya amsa laifi guda daya, yayin da Shaibu ya amsa laifuka biyu a gaban kotun.
A wani bangaren kuma, Mai shari’a Omotosho ya yanke wa Shamsudeen Muhammad Ibrahim, wanda aka fi sani da Abu Harira, hukuncin daurin rai da rai.
An kuma kara masa daurin shekaru 35 a wani laifi daban, wanda zai fara aiki daga ranar 18 ga Yunin 2026.
An same shi da laifin tallafa wa kungiyar ISWAP ta hanyar karbar horo da wa’azi masu goyon bayan ayyukan ta’addanci.
Sojoji sun ragargaji yan ta'adda a Borno
An ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare ta sama kan maboyar 'yan ta'adda a jihar Borno, inda suka hallaka da dama daga cikinsu.
Sojojin sun kai hare-haren ne wadanda suka yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda a maboyarsu da ke yankin Tumbuns na jihar Borno.
Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar ceto wasu mutane da suka hada da maza da mata wadanda 'yan ta'adda suka yi yunkurin sacewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

