Ana Wasan Sauya Sheka a Gombe, Sakataren ADC Ya Yi Murabus, Ya Kama Layin Pantami

Ana Wasan Sauya Sheka a Gombe, Sakataren ADC Ya Yi Murabus, Ya Kama Layin Pantami

  • Sakataren ADC na ƙaramar hukumar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar tare da komawa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya
  • Ya ce ya sauya sheka ne saboda ya yi imanin Pantami na da ƙwarewa, gogewa da nagartar jagoranci wajen ciyar da Gombe gaba
  • Sauyin sheƙar tasa na daga cikin jerin sauye-sauyen siyasa bayan Pantami ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe ta yi babban kamu bayan karbar sakataren ADC yayin da ake shirin zabe.

Sakataren jam'iyyar ADC na ƙaramar hukumar Gombe, Hon. Babangida Usman, wanda aka fi sani da Babangida Ventures, ya yi murabus daga jam'iyyar.

Sakataren ADC ya koma PDP, ya marawa Pantami baya
Sakataren ADC a Gombe, Babangida Usman da ya bar jam'iyyar zuwa PDP. Babangida Ventures.
Source: Twitter

Jigon ADC ya dawo layin Pantami a Gombe

Rahoton The Nation ya ce Ventures ya sauya sheƙa zuwa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami baya a takararsa ta gwamnan Gombe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Sanata Mohammed Onawo ya fice daga jam'iyyar ADC, ya fito takarar gwamna a zaben 2027

Babangida ya sanar da murabus ɗinsa a Gombe, inda ya tabbatar da cewa ya sauka daga muƙaminsa na sakataren ADC na ƙaramar hukuma kafin ya shiga jam'iyyar PDP a hukumance.

Da yake bayyana dalilin sauya sheƙarsa, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda ya yi imanin cewa Farfesa Pantami na da ƙwarewa, gogewa da halayen shugabanci da ake buƙata domin ciyar da Gombe gaba.

Ya bayyana tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani a matsayin ɗan takarar gwamna mafi nagarta kuma mafi cancanta a zaɓen shekarar 2027, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa gwamnatinsa za ta hanzarta bunƙasa ci gaban Gombe.

A cewarsa, shawarar komawa PDP ta samo asali ne daga burinsa na ba da gudunmawa wajen tabbatar da burin Pantami na zama gwamnan Gombe tare da kawo sauyi mai amfani ga jihar.

Wannan sauya sheƙa na daga cikin jerin sauye-sauyen siyasa da ake gani a Gombe bayan Pantami ya zama ɗan takarar gwamna na PDP, inda 'yan siyasa da magoya baya daga jam'iyyu daban-daban ke ci gaba da bayyana goyon bayansu gare shi.

Kara karanta wannan

A ba su wuta: Gwamnan Bauchi ya umarci sojoji a shafe 'yan bindiga

Ana sa ran Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne zai riƙe tutar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan Gombe da za a gudanar a shekarar 2027.

Ana sa ran Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne zai riƙe tutar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan Gombe da za a gudanar a shekarar 2027.

PDP ta yi babban rashi a Gombe

Mun baku labarin cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP guda biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar yayin da ake shirin zaben 2027.

Tsohon shugaban karamar hukumar Funakaye, Ibrahim Yusuf, ya ce ya janye kansa daga PDP nan take domin sake shiri kan zaben da ke tafe.

Mataimakin sakataren PDP a jihar Gombe, Mohammed Babani Bajoga, shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar yayin da ake shirin yin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.