Dan Majalisar Tarayya Ya Rasa Tikitin Takara, Kotu Ta Sauya Sunansa da Wani
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke takarar ɗan majalisar tarayya karkashin jam'iyyar APC ana shirin zabe
- Kotun ta ce APC ta kasa gabatar da sahihin sakamakon zaɓen fidda gwani, yayin da shaidun jam'iyyar suka nuna sabani da rashin daidaito
- Alƙali ya umarci INEC ta sake buɗe shafinta domin karɓa da loda sunan Abdugani Arobo a matsayin ɗan takarar APC na zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a ranar Laraba ta soke sunan ɗan majalisar wakilai a cikin ƴan takara.
Kotun ta sakoe takarar dan majalisar mai wakiltar mazaɓar Owo/Ose, Timehin Adeleye.

Source: Original
Kotun ta kuma ayyana Abdugani Arobo a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar, cewar rahoton Punch.
Tun da farko, Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na APC ya tura sunan Adeleye ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) cikin jerin 'yan takarar jam'iyyar. Wannan mataki ya jawo rashin gamsuwa daga wasu jiga-jigan APC da mambobinta a Ondo.
Saboda haka, Abdugani Arobo ya kai ƙara kotu yana ƙalubalantar matakin da APC ta ɗauka, jam'iyyar APC mai mulki da INEC ne suka kasance waɗanda ake ƙara a shari'ar.
A hukuncin da Mai Shari'a Peter Lifu ya yanke, kotun ta bayyana cewa APC ta kasa gabatar da sahihin sakamakon zaɓen fitar da gwani, yayin da hujjojin da jam'iyyar ta gabatar suka cika da rashin daidaito da sabani.
Kotun ta tabbatar da cewa Arobo ne ya lashe zaɓen fidda gwani na kujerar Majalisar Wakilai ta mazaɓar Owo/Ose bayan samun mafi yawan ƙuri'un da aka amince da su.
Alƙalin ya bayyana cewa Arobo ya samu ƙuri'u 7,959 a ƙaramar hukumar Owo da kuma ƙuri'u 2,583 a ƙaramar hukumar Ose a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar ranar 16 ga Mayu, 2026.
Kotun ta ce saboda haka Arobo ne kaɗai ya cancanci a tura sunansa ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takarar APC na kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Owo/Ose.
Haka kuma, kotun ta umarci APC da INEC su riƙa amincewa da Arobo kaɗai a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani, tare da hana su mu'amala da wani daban game da wannan takara.
Bugu da ƙari, kotun ta bayar da umarnin dindindin da ke hana APC, INEC ko wakilansu amincewa da wani ɗan takara banda Arobo kan wannan kujera.
A ƙarshe, kotun ta umarci INEC da ta sake buɗe shafinta na yanar gizo domin karɓa da loda sunan Abdugani Arobo a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a zaɓen Majalisar Wakilai na shekarar 2027.
Dan majalisar APC ya yi nasara a kotu
Mun ba ku labarin cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan karar PDP da ke neman a kwace kujerar ɗan majalisar Benue, Anthony Attah, bayan ya koma APC.
Kotun ta ce kundin tsarin mulki ya bai wa kakakin majalisar Benue da majalisar ikon ayyana kujerar babu kowa, ba kotu ba.
Alkalin ya ce INEC ba za ta iya shirya zaben cike gurbi ba sai bayan majalisar ta ayyana kujerar babu kowa sannan kakaki ya sanar da hukumar.
Asali: Legit.ng

