Gwamnatin Tinubu Ta Fara Shari'ar Daruruwan Wasu da Ake Zargi da Ta'addanci

Gwamnatin Tinubu Ta Fara Shari'ar Daruruwan Wasu da Ake Zargi da Ta'addanci

  • Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da shari’ar da ake yi wa fiye da mutum 600 da ake zargi da ta’addanci a kotunan Abuja
  • Ministan shari'a a Najeriya, Lateef Fagbemi ya ce gwamnati ba za ta yi wasa da matsalar ta’addanci ba, domin tabbatar da tsaron Najeriya
  • Kotu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekaru 15 da 20 bayan sun amsa laifuffukan da suka shafi Boko Haram

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da shari’ar ɗaruruwan waɗanda ake zargi da aikata laifuffukan ta’addanci a Abuja.

An fara sauraron shari’un ne a ranar Litinin 15 ga watan Yunin shekarar 2026 da muke ciki domin sanin makomarsu.

An fara shari'ar waɗanda ake zargi da ta'addanci
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Antoni-Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya bayyana cewa gwamnati ba za ta ɗauki matsalar ta’addanci da wasa ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan kotu ta nemi a soke ADC, Tinubu ya yi kira ga alkalai

Yadda za a gudanar da shari'aun

Fagbemi ne ke jagorantar masu gabatar da ƙara, yayin da Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Shari’a, Aliyu Abubakar, ke jagorantar lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma.

Ana gudanar da shari’un a lokaci guda a kotuna daban-daban, kuma ana sa ran za su ɗauki tsawon mako guda.

Daga cikin alkalan da ke sauraron shari’un akwai Binta Nyako, Emeka Nwite, Musa Liman, James Omotosho, Obiora Egwuatu da Ekerete Akpan.

Aƙalla mutum 58 da ake zargi da ta’addanci ne aka jera domin gurfana a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a ranar Litinin 15 ga watan Yunin 2026.

Wasu daga cikinsu sun haɗa da Abba Bukar, Abba Manye, Gujja Mala Bukar, Brem Gonimi, Isa Mohammed, Lawali Dashiri Danke, Yau Tukur da Bello Liman.

Sababbin shari’un sun biyo bayan wadda aka gudanar watanni biyu da suka gabata, inda aka yi wa kusan mutum 500 shari’a daga ranar 7 zuwa 10 ga watan Afrilun 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: An samu matsala a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai

An gurfanar da wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci a kotu
Taswirar birnin Abuja da aka fara shari'ar daure wasu da ake zargi da ta'addanci. Hoto: Legit.
Source: Original

Alwashin gwamnatin Tinubu kan ayyukan ta'addanci

Da yake zantawa da manema labarai, Fagbemi ya ce shari’un na nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da ta’addanci da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

Ya ce sakon da gwamnati ke son isarwa a bayyane yake, cewa ba za a lamunci ta’addanci ta kowace irin siga ba, cewar Daily Post.

Fagbemi ya bayyana cewa wannan shi ne zagaye na huɗu na irin waɗannan shari’u tun bayan hawan gwamnatin da ke mulki.

Ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa Najeriya ta zama ƙasa mai aminci ga kowa.

A cewarsa, a wannan zagayen akwai kusan mutum 490 a ranar Litinin, sannan za a gurfanar da mutum 84 a washegari.

Ya ƙara da cewa wannan adadin bai haɗa da mutum 102 da aka ɗauko daga zagayen baya ba, ya ce adadin waɗanda za a yi wa shari’a a wannan zagaye ya zarce mutum 600.

Kara karanta wannan

Janar Rabe: Buratai ya yi gargadi kan 'sace' gwamnoni da ministoci a Najeriya

Wannan shari’ar gama-gari wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na gurfanar da waɗanda ake zargi da ta’addanci, tayar da ƙayar baya da sauran laifuka masu alaƙa da rashin tsaro.

A gefe guda kuma, an samu nasarar yanke hukunci kan wasu mutum biyu bayan sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.

Rashin tsaro: Katsina ta hana POS, cajin waya

An ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya dauki sababbin matakai domin inganta tsaro da magance matsalar 'yan bindiga masu sace jama'a.

Lamarin ya biyo bayan matakan da hukumomi suka ce za su dauka bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) a hannun masu garkuwa a jihar.

Daga cikin matakan tsaro da gwamnati dauka akwai hana sana'ar POS da cajin waya a wasu kananan hukumomin jihar da rashin tsaro ya yi kamari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.