CUPP Ta Goyi bayan Wasu Yan Majalisa da Suka ba Shugaba Tinubu Zabi 1 ko Ya Yi Murabus
- Gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya (CUPP) ta goyi bayan kiran da ƴan Majalisar Wakilai na tsagin adawa suka yi ga Shugaba Bola Tinubu
- Kungiyar ta bayyana cewa kamata ya yi duk shugaban da ya kasa samar da ingantaccen shugabanci ya sauka daga mulki cikin mutunci
- Ta bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa kan tsaro da matsin tattalin arziki domin shawo kan matsalolin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gamayyar jam'iyyun siyasa a Najeriya (CUPP) ta bayyana goyon bayanta ga kiran da ƴan Majalisar Wakilai na tsagin adawa suka yi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ya dauki matakai ko ya yi murabus.
Mukaddashin Shugaban CUPP na kasa Cif Peter Ameh, ne ya bayyana matsayar kungiyar a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan
Mutuwar Janar Rabe: Kwankwaso ya kai ziyara Katsina, ya bada mafita kan matsalar tsaro

Source: Twitter
Ya ce matsayar gamayyar jam’iyyun adawar ta yi daidai da ra’ayin ƴan majalisar wakilai na tsagin jam'iyyun adawa, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Tun farko, yan Majalisar wakilan sun bukaci Tinubu ya jagoranci kasar nan yadda ya kamata ta hanyar daukar matakan kare rayukan yan Najeriya ko kuma ya yi murabus.
CUPP ta bai wa Bola Tinubu zabi 2
Da take goyon bayan yan Majalisar, CUPP ta nuna cewa wajibi ne gwamnatin da ke mulki ta fuskanci kalubalen da ke addabar ƴan Najeriya ko kuma ta bai wa wasu damar jagoranci.
Ameh ya ce a kowace kasa mai mutunta tsarin dimokuradiyya, duk wani zababben shugaba da ya kasa samar da sakamakon da zai inganta rayuwar al’umma, ya kamata ya sauka daga mukaminsa cikin mutunci.
“Duk wani zababben jami’i da ya kasa samar da ingantaccen shugabanci da zai kyautata rayuwar jama’a ya kamata ya yi murabus cikin girmamawa,” in ji Ameh.

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun gano abin da ke kullawa domin sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Matakan da ake so Tinubu ya dauka
CUPP ta bukaci Tinubu da gwamnatinsa su dauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro, tsadar rayuwa da kuma halin kuncin tattalin arziki da ƴan Najeriya ke fuskanta.
A cewar kungiyar, shugabanci nauyi ne, ba gata ba, inda ta kara da cewa:
“Shugabanci ba hakki ba ne, nauyi ne. Idan ba a sauke wannan nauyi yadda ya kamata ba, hanya mafi dacewa ita ce yin murabus."

Source: Twitter
Kungiyar ta sake tabbatar da kudirinta na ci gaba da fafutukar ganin an samar da nagartaccen shugabanci, gaskiya da rikon amana tare da kare muradun ƴan Najeriya.
Ta kuma bukaci shugaban kasa da ya saurari wannan kira tare da daukar matakai masu gamsarwa domin rage radadin halin da jama’a ke ciki a fadin kasar nan, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Wasu yan Majalisa sun taso Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa yan majalisar wakilai na jam'iyyun adawa sun ba da shawara kan yadda ya kamata gwamnatin tarayya ta tunkari matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan
An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya
Sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana wani shiri na watanni shida domin dawo da zaman lafiya da walwalar jama'a.
Yan majalisar ta bakin shugaban marasa rinjaye, Hon. Fred Agbedi, sun bukaci shugaba Tinubu ya dauki matakan da ya dace ko kuma ya yi murabus.
Asali: Legit.ng