Sarkin Musulmi, Shugabannin Kirista Sun Yi Kira da Murya Daya kan Matsalar Tsaro
- Sarkin Musulmi da shugabannin Cocin Katolika sun nuna damuwa kan karuwar kashe-kashe da garkuwa da mutane a fadin Najeriya
- Sun bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro da ke addabar al’ummar kasar
- Bangarorin biyu sun jaddada bukatar hadin kai tsakanin jama'a, gwamnati da jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya da aminci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Manyan shugabannin Musulunci da Katolika a Najeriya sun bayyana matukar damuwa kan tabarbarewar tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan.
Sarkin Musulmi kuma shugaban kungiyar JNI, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, da kungiyar limaman Katolika (CBCN) sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara kaimi wajen dakile kashe-kashe, sace-sacen mutane da sauran laifuffuka.

Source: UGC
Kiran Sarkin Musulmi ga 'yan Najeriya
Kiran nasu ya zo ne bayan hare-haren da ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai suka kai a wasu yankunan kasar, musamman a Arewacin Najeriya, in ji rahoton Premium Times.
A sakonsa na sabuwar shekarar Musulunci ta 1448AH, Sarkin Musulmi ya bukaci ‘yan Najeriya su hada addu’a da goyon bayan jami’an tsaro domin shawo kan matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da sakataren JNI, Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, Sarkin Musulmin ya ce magance matsalar tsaro aiki ne da ya rataya a wuyan gwamnati, shugabannin addini da kuma al’umma baki daya.
“Lokaci ya yi da za mu sake komawa ga Allah tare da hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa,” in ji shi.
Domin neman taimakon Ubangiji, Sarkin Musulmi ya umarci limaman masallatai a fadin kasar nan su rika gudanar da addu’ar Qunootun-Nawazil, wadda ake yi a lokutan bala’i da matsin rayuwa.
Limaman Katolika sun nuna damuwa
A nasa bangaren, Archbishop na Legas kuma mataimakin shugaban CBCN, Alfred Martins, ya ce ‘yan Najeriya na kara shiga damuwa sakamakon yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma raba jama’a da muhallansu.
Martins ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron godiya da aka gudanar a Holy Cross Cathedral da ke Legas domin murnar cika shekaru 90 da haihuwar Anthony Okogie.
Ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni da aka zaba su kara kokari wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.
“Kullum muna jin labarin sace mutane, kashe sojoji, korar al’umma daga gidajensu da kuma sarakunan gargajiya da ke tserewa daga yankunansu. Wannan lamari ya zama abin damuwa sosai,” in ji Martins.

Source: Twitter
An bukaci kara tallafa wa jami’an tsaro
Faston ya kuma bukaci gwamnati ta kara inganta walwala, kayan aiki da kwarin gwiwar jami’an tsaro domin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ko da yake ya yaba da wasu matakan da gwamnati ke dauka, Martins ya ce mutane da dama na ganin matsalar tsaro na ci gaba da tsananta duk da kokarin da ake yi na magance ta.
Abin da ke rura wutar rashin tsaro
A wani labari, mun ruwaito cewa, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya yi karin haske kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Mai alfarma Sarkin Musulmin ya nuna illar da ke tattare da yin watsi da matasa wadanda ke rayuwa a cikin al'umma ba tare da samar musu da abin dogaro da kai ba.
Hakazalika babban basaraken ya bayyana cewa karfafa matasa ta hanya koya musu sana'o'i ba karamin amfani zai yi wa al'umma ba.
Asali: Legit.ng

