Sojoji Sun Sada Idi Abasu Aiki da Wasu 'Yan Bindiga 60 da Mahaliccinsu a Katsina

Sojoji Sun Sada Idi Abasu Aiki da Wasu 'Yan Bindiga 60 da Mahaliccinsu a Katsina

  • Hukumar DSS tare da jami'an tsaro na sa kai sun yi nasarar hallaka kasrugumin jagoran 'yan bindiga Idi Abasu Aiki bayan wata arangama a jihar Katsina
  • Rahotanni sun ce fiye da 'yan bindiga 200 ne suka kai hari Guga da nufin ramuwar gayya kan al'ummomin da ke taimaka wa masu tsaron sa-kai
  • Jami'an sun kuma yi nasarar kwato makamai da sauran kayayyaki da 'yan bindigar suka bari, amma duk da nasarar an samu asarar rayukan zaratan ma'aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tare da hadin gwiwar 'yan sa kai da mafarauta na musamman sun kashe sama da 'yan bindiga 60.

An samu wannan nasara ne a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Ana zargin ƴan jagaliyar APC sun yi wa mambobin PDP jina jina a taron sauya sheƙa

SSS da jami'an sa kai sun yi nasarar hallaka uban dabar yan bindiga a Katsina
Wasu daga cikin sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Zagazaola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa fitaccen jagoran 'yan bindiga, Idi Abasu Aiki, wanda ake zargi da jagorantar hare-hare da dama a jihohin Katsina da Zamfara, na cikin wadanda aka kashe a wannan farmaki.

Yadda aka yi dauki ba dadi a Katsina

The Nation ta kawo labarin cewa a cewar majiyoyin, jami'an sa kai da mafarauta sun taimaka wajen gudanar da aikin, sai dai mutum hudu daga cikinsu sun rasa rayukansu yayin artabun da 'yan bindigar.

Wata majiya ta ce:

"Fiye da 'yan bindiga 200 dauke da makamai karkashin jagorancin Idi Abasu Aiki sun mamaye kauyen Guga da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina."
An kuma hallaka yan bindiga 60 bayan jagoransu
Taswirar jihar Katsina inda aka gwabza da yan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Majiyar ta kara da cewa:

"Sun samu taimakon wasu 'yan bindiga daga kungiyar Ado Aleru da ke jihar Zamfara, kuma sun fito ne domin kai hari kan al'ummomin da suke zargin suna goyon bayan rundunar tsaron jihar da ke kare kauyukan yankin."

Kara karanta wannan

An tsinci gawar malami a yashe, an ce wasu ne suka daɓa masa wuka har lahira

Ana raunana yan bindiga a Katsina

Rahoton ya ce a watan da ya gabata 'yan bindigar sun yi asara mai yawa a kauyen Dawan Laila a hannun mafarauta, lamarin da ya sa suka shirya komawa domin ramuwar gayya tare da rusa kungiyar tsaron al'umma kafin su kai hare-hare kan sauran kauyuka.

Sai dai majiyar ta bayyana cewa DSS ta riga ta samu cikakken bayanan sirri game da shirin nasu kuma an yi masu kyakkyawan shiri na tarbarsu.

Wata majiyar tsaro ta kuma ce bayan kammala artabun, jami'an DSS da sauran jami'an tsaro sun gudanar da aikin share fage inda suka kwato makamai da sauran kayayyakin da 'yan bindigar suka yi watsi da su.

NAF ta karbi kayan yaki da yan bindiga

A baya, mun kawo labarin cewa sojojin saman Najeriya (NAF) sun kammala bincike na ƙarshe na karɓar rukunin farko na jiragen yaƙi guda uku samfurin M-346 daga ƙasar Italiya domin taimaka wa bangaren tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun magantu, sun tsuga miliyoyi na fansar alkalin babbar kotun Kebbi

Wannan mataki zai taimaka sosai wajen inganta ƙwararrun ma'aikata da kuma ɗaga darajar NAF wajen kai hare-hare cikin sauri da kare ƙasa daga farmakin yan ta'adda da sauran bata gari da ke addabar jama'a.

Wannan na zuwa ne a zamanin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wani ɓangare na kokarin zamantar da kayan aikin soji na ƙasa domin tukarar matsalolin rashi tsaro da ake fama da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng