An Yanke wa Hauwa'u Mukhtar Hukuncin Kisa, za a Rataye Ta a Katsina kan Ta'addanci

An Yanke wa Hauwa'u Mukhtar Hukuncin Kisa, za a Rataye Ta a Katsina kan Ta'addanci

  • Babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci
  • Kotun ta samu matar da laifin safarar harsasai 438 zuwa wani shugaban ‘yan bindiga da ke maboyarsa a dajin Dunburum
  • Hukumar DSS ta kama Hauwa’u Mukhtar a tashar mota ta Jibia a shekarar 2023 yayin da ake zargin tana kai harsasai Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifuffukan da suka shafi ta’addanci.

Mai shari’a A.B. Bawale ne ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da cewa an same ta da laifin hada baki da kuma taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda.

Kotu ta yanke wa wata mata hukuncin kisa kan taimaka wa 'yan ta'adda a Katsina.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shari'ar matar da ke safarar alburusai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shari'ar daruruwan wasu da ake zargi da ta'addanci

Kotun ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi mata ba tare da wata shakka ba, a cewar rahoton Daily Trust.

Bayanan kotu sun nuna cewa jami’an DSS sun kama Hauwa’u Mukhtar ne ranar 16 ga watan Satumban 2023 a tashar mota ta Jibia da ke jihar Katsina.

Ana zargin tana kokarin kai harsasai guda 438 na bindigar AK-47 mai girman 7.62mm ga wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Ado.

Rahotanni sun ce ana kyautata zaton shugaban ‘yan bindigar na boye ne a dajin Dunburum da ke jihar Zamfara.

Bayan kama ta, hukumar DSS ta gurfanar da ita a gaban kotu kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da hada baki wajen aikata ta’addanci da kuma taimakawa ayyukan ‘yan ta’adda.

Kotun ta yanke mata hukuncin kisa

A yayin sauraron shari’ar, kotun ta saurari bayanan shaidu da kuma hujjoji da masu gabatar da kara suka gabatar domin danganta matar da safarar harsasan zuwa hannun ‘yan bindiga.

Da yake yanke hukunci, mai shari’a Bawale ya bayyana cewa kotun ta yi nazari sosai kan dukkan hujjojin da aka gabatar.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka da wani bam ya tarwatse da motar sulken 'yan sanda a jihar Zamfara

Daga bisani kotun ta same ta da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ake yi mata tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa dokar Penal Code ta jihar Katsina ta shekarar 2021.

An kama matar da aka yanke wa hukunci ne dauke da alburusai fiye da 400 za ta kai wa 'yan bindiga a Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara, inda aka yanke wa wata mata hukuncin kisa kan alaka da 'yan bindiga. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mahangar masana tsaro kan hukuncin

An bayyana hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki a yunkurin hukumomin tsaro da bangaren shari’a na dakile matsalar ta’addanci, safarar makamai da ayyukan ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Masana harkokin tsaro sun sha bayyana cewa safarar makamai da harsasai na daga cikin manyan abubuwan da ke kara karfin ‘yan bindiga wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin, in ji rahoton PM News.

Wannan hukunci na zuwa ne makonni biyu bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa wasu mutane hudu hukuncin kisa kan harin cocin St. Francis Catholic da ke Owo a jihar Ondo a shekarar 2022.

An kama wata mata da harsasai 991

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun yi nasarar kama wata mai yi wa yan bindiga safarar makamai a jihohin arewa maso yamma da tsakiya.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: An samu matsala a shari'ar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai

An kama Fatima Lawali ne mai shekaru 30 dauke da harsahi guda 991 na AK-47 za ta kai wa wani dan bindiga mai suna Ado Alero a Zamfara.

Kwamshinan 'yan sanda CP Ayuba Elkanah na lokacin ya ce an kwace makaman sannan tuni an fara bincike a kan lamarin idan an gama za a gurfanar da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com