'Zabe ne a Gabansa': Yan Majalisa Sun Dura kan Tinubu game da Tsaron Ƙasa

'Zabe ne a Gabansa': Yan Majalisa Sun Dura kan Tinubu game da Tsaron Ƙasa

  • 'Yan Majalisar Wakilai sun caccaki gwamnatin Bola Tinubu game da matsalolin tsaro da ke faruwa a Najeriya
  • Sun nuna damuwa kan kisan Manjo Janar mai ritaya Rabe Abubakar bayan sace shi tare da matarsa a Katsina
  • Mambobin sun kuma soki hukuncin kotu kan soke rajistar wasu jam’iyyun adawa, suna mai cewa hakan na iya raunana adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƴan Majalisar Wakilai sun dura kan gwamnatin Bola Tinubu game da karuwar matsalolin tsaro a Najeriya.

Mambobin sun zargi gwamnatin tarayya da sakaci da mayar da hankali kan babban zaɓen 2027.

Yan majalisa sun caccaki Tinubu kan rashin tsaro
Mambobin majalisar dokokin Najeriya da shugaba Bola Tinubu. Hoto: House of Representatives, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin jawabin shugaban marasa rinjaye, Hon. Fred Agbedi yayin taro a Abuja, cewar rahoton Punch.

Rabe: Yan majalisar tarayya sun yi Allah-wadai

Agbedi ya ce Najeriya na fuskantar haɗarin matsalolin tsaro, ƙuncin rayuwa da kuma barazana ga dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Sun nuna takaici kan kisan Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya wanda aka ce an sace shi tare da matarsa a Katsina kafin daga baya aka sanar da mutuwarsa.

Agbedi ya bayyana lamarin a matsayin babban bala’i ga ƙasa, yana mai cewa mutuwar tsohon hafsan sojan ta nuna yadda gwamnati ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya ce abin takaici ne yadda tsohon janar na rundunar sojin Najeriya da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare ƙasa ya gamu da wannan mummunan yanayi.

Yan majalisar suka ce kisan ya biyo bayan mutuwar wasu manyan jami’an tsaro a yaƙi da masu tayar da ƙayar baya, lamarin da ke nuna yadda rashin tsaro ke ƙara yaɗuwa.

An taso Tinubu a gaba kan matsalar tsaro
Shugaba Bola Tinubu ya yi tagumi yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ƴan adawa: Matsayar yan majalisar kan hukuncin kotu

A bangaren siyasa kuwa, sun soki hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyun adawa guda biyar, cewar TheCable.

Ta ce hukuncin na iya haddasa ruɗani a tsarin siyasar ƙasa, tare da haifar da zargin cewa ana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.

Agbedi ya ce hukuncin ya saɓa da wani hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, kuma bai yi la’akari da bayanan da INEC ta gabatar ba.

Kara karanta wannan

Dakarun gandun daji: Tinubu amince a dauki sababbin ma'aikata 1,000 a Katsina

Ya bayyana hukuncin a matsayin wani yunƙuri na fitar da jam’iyyun adawa daga fafatawar neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Agbedi ya jaddada cewa rayuwar kowane ɗan Najeriya tana da muhimmanci, yana mai cewa siyasa ya kamata ta koma baya yayin da ƙasa ke fuskantar matsaloli.

Daga cikin buƙatunsu akwai sake fasalin tsarin tsaron ƙasa gaba ɗaya, gudanar da bincike mai gaskiya kan kisan Janar Rabe, da kuma warware rikice-rikicen hukuncin kotuna.

Haka kuma sun buƙaci Shugaba Tinubu ya dakatar da duk wasu shirye-shiryen da suka shafi zaɓen 2027, ya mayar da hankali kan shirin watanni shida na farfaɗo da tsaro da tattalin arziki.

An fara shari'ar 'yan ta'adda' 600 a Najeriya

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da shari’ar da ake yi wa fiye da mutum 600 da ake zargi da ta’addanci a kotunan Abuja.

Ministan shari'a a Najeriya, Lateef Fagbemi ya ce gwamnati ba za ta yi wasa da matsalar ta’addanci ba, domin tabbatar da tsaron Najeriya.

Kotu ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin daurin shekaru 15 da 20 bayan sun amsa laifuffukan da suka shafi Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.