Peter Obi Ya Ware Rukunin 'Yan Bindigan da Zai Yi Sulhu da Su idan Ya Zama Shugaban Kasa a 2027

Peter Obi Ya Ware Rukunin 'Yan Bindigan da Zai Yi Sulhu da Su idan Ya Zama Shugaban Kasa a 2027

  • 'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta hada da sulhu da matakan tsaro wajen magance rashin tsaro
  • Obi ya bayyana tsarin da zai bi wajen kawo karshen matsalar 'yan bindiga idan ya samu nasarar zama shugaban kasa a zaben 2027
  • Tsohon gwamnan Anambra ya ce samar da zaman lafiya mai dorewa na bukatar tattaunawa da mutanen da suka nuna aniyar rungumar sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana tsarin da zai bi wajen dawo da zaman lafiya idan aka zabe shi shugaban kasa a 2027.

Ya ce gwamnatinsa za ta bude kofar tattaunawa da ’yan bindiga da sauran kungiyoyin masu tada kayar baya da suka shirya rungumar sulhu tare da daina aikata miyagun laiffuffuka.

Kara karanta wannan

Kungiyar musulmi ta goyi bayan mafitar da Matawalle ya kawo kan matsalar tsaron Najeriya

Peter Obi.
'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin BlackBox tare da Rufai Oseni, inda ya yi bayani kan yadda zai magance matsalolin tsaro da hada kan kasa idan ya hau mulki.

Bayan yunkurin sulhu, Peter Obi ya kuma lashi takobin yin amfani da karfi kan yan ta'addan da suka dage sai sun ci gaba da tayar da hankali da aikata miyagun laifuffuka.

Peter Obi ya fadi shirinsa kan tsaro

Tsohon gwamnan Anambra ya ce samar da zaman lafiya mai dorewa na bukatar tattaunawa da mutanen da suka nuna aniyar rungumar sulhu da bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.

“A kokarin hada kan Najeriya, duk wanda yake son zaman lafiya zan yi magana da shi, zan tattauna da shi. Duk wanda yake son yaki kuma, za mu yake shi,” in ji Obi.

Ya kara da cewa Najeriya na bukatar samar da hanyoyin gyara da dawo da mutanen da suka tuba daga aikata laifuffuka domin su zama masu amfani ga al’umma.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

Ya ba da misali daga Amurka

Domin karfafa hujjarsa, Obi ya ba da misalin wata jami’a da ya ziyarta a Amurka, inda ya ce wasu daga cikin manyan jami’an makarantar sun taba zaman gidan yari kafin daga bisani suka gyara rayuwarsu.

Obi ya ce:

“Na taba ziyartar wata jami’a a Amurka inda mafi yawan shugabannin makarantar sun taba shiga gidan yari saboda wasu laifuffuka. Amma daga baya suka canza rayuwarsu suka zama malamai da shugabanni.”
Peter obi.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi yana jawabi a wurin wani taro Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

A cewarsa, idan mutum ya nuna gaskiyar niyyar canzawa, ya kamata a ba shi damar sake farawa, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Dan takarar shugaban kasar ya danganta matsalar tsaro da rashin wakilci nagari a wasu sassan kasa, yana mai cewa dole ne kowane yanki da kabila su ji cewa suna da gurbi a harkokin mulki da ci gaban kasa.''

Peter Obi zai saki Nnamdi Kanu

A wani labarin, an ji cewa dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi ya ce zai saki shugaban kungiyar fafutukar ballewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu idan ya samu nasara a 2027.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

Ya kuma ce zai shiga tattaunawa da masu fafutukar ballewa da sauran masu korafe-korafe a fadin Najeriya domin fahimtar dalilansu da kuma warware matsaloli ta hanyar zaman lafiya.

Obi ya jaddada cewa tattaunawa da fahimtar juna ne kadai hanyar warware matsalolin masu fafutuka da rikice-rikicen cikin gida a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262