Bayan Davido, Rarara Ya Dura kan Malaman Arewa Masu Wa'azi kan Rashin Tsaro

Bayan Davido, Rarara Ya Dura kan Malaman Arewa Masu Wa'azi kan Rashin Tsaro

  • Mawakin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga malaman addinin Musulunci da su gyara salon wa'azinsu game da matsalar tsaro
  • Dauda Rarara ya bayyana cewa ya kamata malaman kasar nan su fara wa'azi game da masu yada bidiyon 'yan ta'adda a kafafen sadarwa
  • Ya kara da cewa ya dade yana sane da abin wasu malamai suke fada game da shi, ba ya mayar da martani ne saboda shi ma mahaifisa malami ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Fitaccen mawakin jam'iyyar APC a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana kan yadda wasu malaman addini ke wa'azi.

Mawakin ya ce wasu malamai sun koma neman mabiya a kafafen sadarwa maimakon jan hankalin al'umma game da abaubuwan da suka kamata.

Kara karanta wannan

Rarara ya fadi dalilin da yasa ba zai yi wa Davido martani da Turanci ba

Mawaki Dauda Kahutu Rarara
Mawakin APC, Dauda Rarara sanye da hular tallan Bola Tinubu. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da DCL Hausa ta wallafa a Facebook, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa shi ma zai iya irin wa'azin da wasu ke yi da sunan malanta.

Kiran Dauda Rarara ga malaman addini

A hirar da aka yi da shi, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa yawanci matsalar tsaro ta dawo ita ce abin da suke wa'azi a kanta a kullum.

Ya kara da cewa wasu malamai sun kyale wa'azi sun koma barkwanci suna tsine wa mutanekan tsaro kuma bayan sun sani duk wanda suka zaga idan bai yi martani ba za ta dawo kansu.

Rarara ya ce duk da shi ba malami ba ne, shi kolo ne, amma duk da haka yana kira ga malamai da su rika kira ga 'yan soshiyal midiya kan saka bidiyon 'yan ta'adda.

Mawakin ya bayar da misali da cewa yadda aka rika yada matsalar Janar Rabe Abubakar da aka sace ta kara jefa tsohon sojan cikin matsala.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya yi magana kan kama dan ta'adda Bello Turji

Rarara ya ce abin takaici shi ne:

"To malama ne za su mana wannan aikin, to su ma malaman sun koma neman mabiya."

Alakar Rarara da malaman Musulunci

Dauda Rarara ya bayyana cewa wasu malamai sun dade suna zagin shi amma duk da haka ba zai mayar masu da martani.

'Wasu malamai suna zagi na, amma ban taba martani ba, ka san baba na malami ne, ba zan mayar wa iyayena martani ba."

Duk da haka, ya ce yana ba su shawara da su rika kira ga masu yada bidiyo a intanet su daina watsa bidiyon da 'yan ta'adda suka yi.

Dauda Kahutu Rarara
Dauda Rarara tare da wasu masu alaka da sarauta. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Rarara ya kara da cewa duk da shi ba wani mai ilimi ba ne sosai, zai iya irin wa'azin da wasu malamai suke yi na jawo aya ko hadisi daya su yi ta sukar jama'a.

Rarara ya gargadi Davido

A wani labarin, mun kawo muku cewa mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana kan wata riga da fitaccen mawaki Davido ya saka a Amurka.

Kara karanta wannan

Rarara ya dawo da batun sace mahaifiyarsa, ya caccaki Atiku bayan Davido

Rarara ya ce sanya riga mai dauke da sunayen dalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo a wajen taron kofin duniya da Davido ya yi abin kunya ne.

Ya kuma bayyana cewa hakan taimakon 'yan ta'adda da ke satar mutane ne a kasar nan ne, domin ya kara yada ayyukan su a fadin duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng