Mutuwar Janar Rabe: Kwankwaso Ya Kai Ziyara Katsina, Ya bada Mafita kan Matsalar Tsaro

Mutuwar Janar Rabe: Kwankwaso Ya Kai Ziyara Katsina, Ya bada Mafita kan Matsalar Tsaro

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Kwankwaso ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi Janar Rabe Abubakar mai ritaya
  • Yayin wannan ziyara da ya kai jihar Katsina, Kwankwaso ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsalar Najeriya
  • Jagoran tafiyar kwankwasiyayya, ya ce gwamnatin NDC za ta fifita tsaro, samar wa matasa ayyukan yi da shugabanci nagari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su kara kaimi wajen magance matsalar tsaro a jihar Katsina da sauran sassan Najeriya.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Katsina ranar Laraba yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a wata ziyarar ta'aziyya da ya kai kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Kwankwaso.
'Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Kwankwasi yayin da ya je ta'aziyya gidan marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar a Katsina Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Rabi'u Kwankwaso ya kawo mafita kan tsaro

A rahoton da The Nation ta ruwaito, tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce matsalar tsaro ita ce babbar kalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Kwankwajso ya yi kira ga dukkan matakan gwamnati da su dauki matakai masu inganci domin kawo karshen ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuffuka.

"Wannan matsalar tsaro tana da matukar muhimmanci. Ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su yi duk mai yiwuwa domin kawo karshen rashin tsaro da ayyukan ’yan bindiga a Najeriya," in ji shi.

Kwankwaso ya yaba wa marigayi Rabe

Kwankwaso ya bayyana marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar a matsayin jarumin soja wanda ya yi wa Najeriya hidima da kwarewa, sadaukarwa da kishin kasa.

Ya yi addu'ar Allah Ya ji kansa da rahama tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

Alkawarin NDC kan tsaro a Najeriya

Tsohon gwamnan Kano ya ce idan NDC ta samu damar jagorantar kasar nan, za ta mayar da hankali wajen inganta tsaro, samar da damarmaki ga matasa da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

Ya kuma bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Peter Obi, da kungiyar Obedient Movement suna da buri iri daya da na Kwankwasiyya wajen samar da ingantaccen shugabanci da ci gaban kasa.

Kwankwaso.
Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya bukaci magoya bayan jam'iyyar su kara zage damtse wajen wayar da kan jama'a domin samun nasara a zabuka masu zuwa.

"Burinmu shi ne ganin matasanmu sun cimma mafarkansu ta hanyar zama likitoci, injiniyoyi, matukan jirgi, ’yan kasuwa masu nasara da kwararru a fannoni daban-daban."
"Muna son ganin Najeriya ta fi yadda take a yanzu, kuma wannan ne ya sa muka kuduri aniyar ci gaba da wannan gwagwarmaya," in ji shi.

Kwankwaso ya bude kofar sulhu da Abba

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sake magana kan alakar shi da Abba Kabir Yusuf da ya lashe zaben gwamnan Kano a 2023.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Kwankwaso ya bayyana cewa ba korar Abba Kabir Yusuf ya yi ba a tafiyar Kwankwasiyya, shi gwamnan ne ya tafi ba tare da izinin shi ba.

Madugu ya bayyana cewa a shirye ya ke ya yafe wa duk wani dan Kwankwasiyya da aka samu sabani da shi ciki har da Gwamna Abba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262