Yan bindiga
Akalla mutane 10 aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe malamin addinin Musulunci bayan ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Gidan Kare a jihar Sokoto.
A labarin nan za a ji cewa jami'an tsaro a jihar Kebbi sun samu nasarar tarwatsa gungun tan ta'adda da ke shirin karban fansa, inda aka ceto wata baiwar Allah.
’Yan sandan jihar Zamfara sun kashe ’yan bindiga 17 bayan musayar wuta, yayin da ake ci gaba da kokarin ceto fasinjojin da aka sace a harin Tsafe.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kai dauki bayan samun rahoton tashin bam a kan titin Gurusu zuwa Gwashi da ke karamar hukumar Bukkuyim a Zamfara.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane huɗu, sun sace huɗu tare da jikkata bakwai a Gorau, Sokoto, yayin da ake zargin sun kai hari neman tallafin N1m.
Yan bindiga sun yi garkuwa da dan kasuwa Alhaji Yusuf Keche bayan ya fito daga Sallar Isha’i a Dabi, karamar hukumar Kwali da ke cikin birnin Abuja.
Dakarun sojojin Najeriya sun cafke wani mutum da ake zargi da alaka da ISWAP a jihar Borno bayan gano hotonsa tare da wasu dauke da bindigogin AK-47.
Yan bindiga a Jihar Niger sun saki yara 48 da suka yi garkuwa da su har tsawon makonni uku bayan an biya kudi, inda a yanzu suka koma gida lafiya gaban iyayensu.
’Yan bindiga sun kashe Hakimin Galla, Alhaji Ahmed Yusuf, a Niger bayan ya yi musu gargadi, yayin da Gwamna Bago ya nemi a gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
Yan bindiga
Samu kari