An Shiga Jimami da 'Yan Bindiga Suka Kashe Babban Limami da Wasu Mutane a Sokoto

An Shiga Jimami da 'Yan Bindiga Suka Kashe Babban Limami da Wasu Mutane a Sokoto

  • 'Yan bindiga sun sake kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Hatsabiban 'yan bindigan sun hallaka wani babban limami tare da wasu mutane a hare-haren wadanda suka kai a kauyuka biyu
  • Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kuma yi awon gaba da dabbobi masu dumbin yawa yayin hare-haren da suka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kashe babban limamin kauyen Talluje da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto

'Yan bindigan sun kai harin ne a Talluje da kuma kauyen Chofi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane biyu tare da tilasta wa daruruwan mutane guduwa daga gidajensu.

'Yan bindiga sun kashe babban limami a Sokoto
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce harin wanda ya fara da misalin karfe 4:00 na yamma, ya ritsa da kauyuka biyu da ke gundumar Danchadi kuma ya dauki kusan sa'o'i biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa masu koyon karatun Alkur'ani wuta a Bauchi

Wannan lamari ya kawo adadin manyan limamai da aka ruwaito 'yan bindiga sun kashe a jihar Sokoto zuwa uku a cikin 'yan makonnin da suka gabata.

Yadda 'yan bindiga suka kai harin

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai hare-hare na hadin gwiwa a dukkan kauyukan biyu a lokaci guda, inda suka rika harbi ba kakkautawa kafin su tsere da adadin dabbobin da ba a tantance ba wadanda suka sace.

Wani shugaban al'umma a Danchadi ya bayyana cewa:

“Hare-haren sun fara ne da misalin karfe 4:00 na yamma kuma suka ci gaba har zuwa kusan karfe 6:00 na yamma."
"'Yan bindigan sun kashe babban limamin Talluje da wasu mutane biyu wadanda har yanzu ba a tantance ko su wane ne ba."

'Yan bindiga sun kora dabbobi

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa maharan sun kuma kora dabbobi masu yawa, duk da cewa ba za a iya tabbatar da takamaiman adadinsu ba nan take.

Hakazalika, wani babban jami’in dan sanda, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da harin da kuma kisan babban limamin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari cibiyar NIPSS, an gwabza fada da jami'an tsaro

"Mun samu rahotanni game da harin kuma mun tura jami'an sashen yaki da garkuwa da mutane zuwa yankin saboda akwai fargabar cewa 'yan bindigan za su iya dawowa," in ji jami'in.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewar mazauna yankin, maharan sun shiga kauyukan ne ta kauyen Duma, wanda ke iyaka da karamar Hukumar Tureta, suna tafiya a kan babura.

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani kan lamarin ba amma ya yi alkawarin yin bincike tare da bayar da bayani.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga sun kashe daliban makarantar allo tare da jikkata wasu a wani hari da suka kai kauyen Rafin Ciyawa a jihar Bauchi.

'Yan bindigan sun kuma jikkata wasu mutane shida tare da yin garkuwa da mutum uku a harin wanda suka kai kauyen Rafin Ciyawa da ke karamar hukumar Ningi.

Da farko maharan sun bude wuta kan wasu yara almajirai da ke kwance a ƙofar gidan malaminsu na makarantar allo saboda tsananin zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng