An Cafke Sarakuna 2 da Matansu kan Zargin Alaka da Yan Ta’adda? Gaskiya Ta Fito

An Cafke Sarakuna 2 da Matansu kan Zargin Alaka da Yan Ta’adda? Gaskiya Ta Fito

  • An yi ta yada wasu rahotanni a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa an kama sarakuna biyu bisa zargin garkuwa da mutane
  • Bincike ya tabbatar da cewa wannan labari tsoho ne da aka fara yaɗawa tun shekarar 2025, ba sabon lamari ba ne
  • Rundunar 'yan sandan Kwara da ɗaya daga cikin sarakunan sun musanta zargin, suna cewa babu wani sarki da aka kama kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin Kwara - Wani saƙo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa an kama sarakuna biyu kan zargin alaka da yan ta'adda.

Majiyoyin suka ce an kama Sarkin Alabe da Babanla a Kwara tare da matansu bisa zargin garkuwa da mutane da haɗa baki da 'yan bindiga.

An karyata rahoton cafke sarakuna kan zargin alaka da yan ta'adda
Taswirar jihar Kwara wacce ke cikin jihohi da ke fama da hare-haren yan ta'adda. Hoto: Legit.
Source: Original

Wani shafin Facebook da ake kira GoldmyneTV ya wallafa rahoton cewa an kama sarakunan da kuma matansu da makudan kudi.

Kara karanta wannan

'Yan kwallo sun rasu bayan hadari a Kebbi, gwamna ya ba su miliyoyin Naira

Rahoton da ake yada wa kan cafke sarakuna

Saƙon ya kuma yi iƙirarin cewa jami'an tsaro sun gano Naira miliyan 90 a gidan Sarkin Alabe, sannan aka gano Naira miliyan 30 a asusun bankin matarsa.

Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun kuma nuna cewa rundunar 'yan sandan Kwara da Sarkin Babanla sun musanta zargin, suna cewa babu gaskiya a cikinsa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta bayyana cewa labarin tsohon ƙarya ne da aka sake yaɗawa domin yaudarar jama'a.

Ta ce rundunar na damuwa da yadda wasu ke sake yada irin waɗannan ƙagaggun labarai, saboda suna haddasa fargaba, bata suna tare da raunana amincewar jama'a ga hukumomin tsaro.

Kwara: Binciken gaskiya kan rahoton cafke sarakuna

Sai dai binciken Cable ya nuna cewa wannan labari ba sabon abu ba ne, domin an fara yaɗa shi tun watan Agustan shekarar 2025.

A ƙarshe, binciken ya tabbatar da cewa ikirarin da ke cewa an kama sarakuna biyu a Kwara saboda alaƙa da 'yan bindiga da garkuwa da mutane ƙarya ne, kuma ba shi da tushe.

Kara karanta wannan

Zafi ya shiga Turai yana ta kashe mutane a Faransa da sauran kasashe

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce:

"ba sabon lamari ba ne, illa tsohon ƙarya da aka sake yaɗawa, wanda ya fara yawo a kafafen sada zumunta fiye da shekara guda da ta wuce."

Ejire-Adeyemi ta ce bincike ya nuna cewa rahoton da aka yaɗa a kafafen sada zumunta "ba shi da ko ɗigon gaskiya."

Ta ƙara da cewa:

"Rundunar na nuna damuwa cewa wasu mutane sun sake fito da wannan ƙagaggen labari tare da yaɗa shi, da alama domin su yaudari jama'a, su haifar da fargabar da ba ta da amfani, su bata sunan wasu mutane, tare da raunana amincewar jama'a ga hukumomin tsaro."

Sarki ya mutu a hannun yan bindiga

A baya, kun ji cewa wani basarake da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar Kwara ya rasu duk da cewa iyalansa sun biya Naira miliyan 18 kuɗin fansa.

Lamarin ya tayar da hankali kan ƙaruwar sace-sacen sarakunan gargajiya da manyan mutane a yankin da ke fama da matsaloli a kwanakin nan.

Rahoto ya ce hukumomin tsaro a Kwara sun fara farautar masu garkuwar domin kama su bayan mutuwar basaraken cikin yanayi mai ban tausayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.