Hankula Sun Tashi da 'Yan Bindiga Suka Sace Fasto da Mambobin Cocinsa a Benue
- 'Yan bindiga sun sake yin aika-aika a jihar Benue bayan da suka yi garkuwa da wani fasto da ke jagorantar wani coci
- Hatsabiban 'yan bindigan sun sace faston ne tare da wasu mambobin cocinsa bayan sun kai harin da ya sake jefa mutane cikin firgici
- An mika kokon bara ga jama'a da su yi addu'o'i domin ganin mutanen da aka sace sun kubuta daga hannun 'yan bindiga cikin koshin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Benue - 'Yan bindiga sun sace wani fasto da wasu mambobi biyu na cocinsa a jihar Benue, a daidai lokacin da ake fuskantar fargaba mai girma game da matsalar rashin tsaro a jihar.
Samuel Gbinde fasto ne a cocin Universal Reform Christian Church (URCC), wadda kuma aka sani da Nongu u Kristu u i Ser u sha Tar (NKST).

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce babban sakatare na URCC, Titus Targba, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 30 ga watan Yulin 2026.
Yadda aka sace fasto a Benue
Titus Targba ya bayyana cewa 'yan bindiga sun sace mutanen ne a gidan faston wanda yake a cocin NKST da ke Andyar.
"An yi garkuwa da wadanda abin ya shafa ne daga gidan faston da ke Cocin NKST, Andyar, a yankin Ishan Classis, jihar Benue," in ji shi.
Mista Targba ya yi kira ga mambobin cocin da kuma al'umma baki daya da su gudanar da addu'o'in ganin an saki faston da aka sace da kuma mambobin cocin guda biyu cikin koshin lafiya kuma ba tare da wani sharadi ba.
An yi kira ga gwamnati kan rashin tsaro
Haka kuma ya bukaci jami'an tsaro da gwamnatin jihar Benue da ta tarayya da su dauki matakin gaggawa domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da kamo wadanda ke da alhakin hakan.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
"Muna kara kira ga jami'an tsaro da abin ya shafa, gami da gwamnatocin jihar Benue da na Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, da su dauki matakin gaggawa na gaske domin tabbatar da ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya, da kuma tabbatar da cewa an kamo wadanda ke da alhakin wannan aikin laifin kuma an mika su gaban shari'a."
- Titus Targba
An bukaci hukumomin tsaro su tashi tsaye
Bugu da kari, cocin ta bukaci hukumomi da su dauki mmatakai na kariya tun da wuri na yaki da garkuwa da mutane da sauran manyan laifuffuka, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
"Yana da muhimmanci a kai fadan har maboyar masu laifin, maimakon sai an jira sai bayan an riga aikata wadannan munanan laifuffuma sannan a rika mayar da martani.
- Titus Targba

Source: Original
Wannan garkuwa da mutane na baya-bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar fargabar rashin tsaro a jihar Benue.
'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki wasu 'yan sanda da ke bakin aiki a jihar Rivers.
Jami’an da abin ya shafa suna gudanar da aikin tsaro ne a wani shingen bincike da ke Obiri-Kwere, Obio/Akpor lokacin da aka farmake su.
'Yan sandan uku da aka kashe yayin harin suna aiki ne a karkashin rundunar Aluu Division da ke karamar hukumar Ikwerre ta jihar.
Asali: Legit.ng
