An Saki Sunaye da Hotunan 'Yan Najeriya 124 da Za a Fatattako Su daga Amurka
- Gwamnatin Amurka ta fitar da sunaye da hotunan 'yan Najeriya 124 da ta ce za a kora bayan samunsu da hannu a aikata manyan laifuffuka
- Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta sanya 'yan Najeriyar cikin jerin da ta kira 'mafi munin masu aikata laifuffuka' da ICE ta kama
- Har yanzu hukumomin Amurka ba su bayyana ranar da za su fara korar mutanen ba, amma an yi cikakken bayani kan laifuffukan da suka aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta wallafa sunaye da hotunan 'yan Najeriya 124 da ta ce za a kora daga kasar saboda samunsu da laifin aikata manyan laifuffuka.
An wallafa jerin sunayen ne a shafin Hukumar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ranar Laraba.

Source: Getty Images
Amurka za ta koro 'yan Najeriya 124
Hukumar ta wallafa a shafinta na intanet cewa an sanya mutanen cikin jerin wadanda ta kira "mafi munin masu aikata laifuka" da Hukumar Shige da Fice ta Amurka (ICE) ta kama, in ji rahoton Vanguard.
Sai dai duk da fitar da sunaye da hotunansu, DHS ba ta bayyana ranar da za a fara korarsu zuwa Najeriya ba.
Hukumar ta ce matakin na daga cikin shirin gwamnatin Amurka na ci gaba da tsaurara dokokin shige da fice tare da korar bakin haure da aka samu da aikata manyan laifuffuka.
A cikin sanarwar, DHS ta ce jami'anta da na ICE na aiwatar da alkawarin Shugaba Donald Trump na fara korar bakin haure masu aikata manyan laifuffuka.
Sunayen 'yan Najeriya da za a koro
Jerin sunayen da DHS ta fitar ya hada da: Sunday Adediora, Sunday Kunkushi, Mkpouto Etukudoh, Marcus Unigwe, Olaniyi Ojikutu, Boluwaji Akingunsoye, Ejike Asiegbunam, Emmanuel Mayegun Adeola, Bamidele Bolatiwa, Ifeanyi Nwaozomudoh, Aderemi Akefe, Solomon Wilfred, Chibundu Anuebunwa, Joshua Ineh, Usman Momoh, Oluwole Odunowo, Bolarinwa Salau da Oriyomi Aloba.
Sauran sunayen sun hada da Oludayo Adeagbo, Olaniyi Akintuyi, Talatu Dada, Olatunde Oladinni, Jelili Qudus, Abayomi Daramola, Toluwani Adebakin, Olamide Jolayemi, Isaiah Okere, Benji Macaulay, Joseph Ogbara, Olusegun Martins, Kingsley Ariegwe, Olugbenga Abass, Oyewole Balogun, Adeyinka Ademokunla, Christian Ogunghide, Christopher Ojuma, Olamide Adedipe, Patrick Onogwu, Olajide Olateru-Olagbegi da Omotayo Akinto.
Karin wasu sunayen da za a kora
Haka kuma akwai Kenneth Unanka, Jeremiah Ehis, Oluwafemi Orimolade, Ayibatonye Bienzigha, Uche Diuno, Akinwale Adaramaja, Boluwatife Afolabi, Chinonso Ochie, Olayinka A. Jones, Theophilus Anwana, Aishatu Umaru, Henry Idiagbonya, Okechukwu Okoronkwo, Daro Kosin, Sakiru Ambali, Kamaludeen Giwa, Cyril Odogwu, Ifeanyi Echigeme, Kingsley Ibhadore, Suraj Tairu, Peter Equere, Dasola Abdulraheem, Adewale Aladekoba da Akeem Adeleke.
Sauran mutanen da ke cikin jerin sun hada da Bernard Ogie Oretekor, Abiemwense Obanor, Olufemi Olufisayo Olutiola, Chukwuemeka Okorie, Abimbola Esan, Elizabeth Miller, Chima Orji, Adetunji Olofinlade, Abdul Akinsanya, Elizabeth Adeshewo, Dennis Ofuoma, Quazeem Adeyinka, Ifeanyi Okoro, Oluwaseun Kassim, Olumide Bankole Morakinyo, Abraham Ola Osoko, Oluchi Jennifer da Chibuzo Nwaonu.

Source: Getty Images
Dalilin shirin koro 'yan Najeriyar daga Amurka
Wannan mataki ya biyo bayan sababbin manufofin shige da fice da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta fara aiwatarwa bayan komawarsa mulki a ranar 20 ga Janairu, 2025, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Hukumar DHS ta ce wannan mataki na cika alkawarin da Trump ya dauka a lokacin yakin neman zabensa na fara korar wadanda ta bayyana a matsayin "mafi munin masu aikata laifuka."
Amurka ta koro 'yan Najeriya
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar ICE ta kori ‘yan Najeriya 2,330 daga Amurka a tsakanin shekarar 2014 zuwa farkon 2025.
Kididdigar ICE ta nuna cewa an samu raguwar adadin 'yan Najeriya da aka kora daga Amurka daga 281 zuwa 138 a shekaru 11.
Najeriya ce ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka yawan mutanen da aka kora daga Amurka a cikin shekarun nan da suka gabata.
Asali: Legit.ng


