'Kar Mu Ji, Kar Mu Gani': Atiku Ya Gargadi Gwamnati game da Obi, El Rufa'i

'Kar Mu Ji, Kar Mu Gani': Atiku Ya Gargadi Gwamnati game da Obi, El Rufa'i

  • 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC tiku Abubakar ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da jagororin adawa, Peter Obi da Nasir El-Rufa'i
  • Ya bayyana haka ne a yayin da 'dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya yi ikirarin ana neman rayuwarsa, kuma ba lallai ya kai babban zaben 2027 ba
  • Shi ma Nasir El-Rufa'i na garkame a hannun hukumar ICPC yayin da iyalansa ke kukan an haramta masa ganin likita tare da kama wanda ke kula da lafiyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa kada wani abu ya samu Peter Obi.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu za ta tara matan Kano ta ba su tallafin kayan sana'a

Atiku ya ce ainihin gwajin dimokuraɗiyya ba yadda masu mulki ke amfani da iko ba ne, illa yadda waɗanda ba sa kan mulki ke iya amfani da haƙƙoƙinsu na kundin tsarin mulki cikin aminci.

Atiku ya gargadi gwamnati kan Peter Obi
'Yan takarar shugaban kasa Peter Obi, Atiku Abubakar, da kuma Nasir El-Rufa'i Hoto: Mr. Peter Obi/Atiku Abubakar/Nasir El-Rufa'i
Source: UGC

Jaridar Daily Trust Atiku ya bayyana cewa kuma sake kira ga gwamnatin tarayya da ta saki tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, cikin gaggawa.

Atiku ya gargadi gwamnatin Tinubu

A ruwayar jaridar Punch Atiku ya bayyana cewa, tarihi bai taɓa yi wa gwamnatin da ta fi mayar da hankali kan yaƙar 'yan adawa fiye da kare rayuka da jin daɗin jama'a adalci ba.

Ya ce:

"Kada wani abu ya samu Peter Obi. A saki Malam Nasir El-Rufai. A ceto dukkannin ɗaliban makaranta, malamai da sauran 'yan Najeriya da ke hannun masu garkuwa da mutane. A daina bin 'yan adawa ana kuma fara tunkarar matsalolin da ke janyo wa asarar rayuka."

A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce kare lafiyar kowane jagoran adawa wajibi ne da kundin tsarin mulki ya ɗora wa gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Segalink ya yi maganar da ka iya zama barazana ga takarar Peter Obi da Kwankwaso a 2027

Atiku ya ce bai dace a rika muzgunaw jagoroin adawa ba
Atiku Abubakar da shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Atiku Abubakar/Peter Obi
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa:

"Kada wani abu ya samu Peter Obi. Cutar da mutum ɗaya tamkar cutar da kowa ce. Idan aka tsoratar da jagoran adawa guda ɗaya, an raunana muryar dukkannin 'yan adawa. Idan ɗan ƙasa ya fara jin tsoro saboda ra'ayinsa na siyasa, to dimokuraɗiyya ce ke shan wahala."

Atiku ya soki martanin shugaban kasa

Atiku Abubakar ya bayyana damuwarsa kan yadda fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga kalaman Peter Obi da zarge-zarge da kalamai na cin mutunci maimakon nuna nutsuwa da ya dace da gwamnatin dimokuraɗiyya.

A cewarsa:

"Ba 'yan adawa ne maƙiyan Najeriya ba. Talauci ne da yunwa da rashin tsaro su ne makiyan kasar."

Ya ce yayin da 'yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro, iyalai da dama na ci gaba da jiran dawowar 'yan uwansu da aka sace.

Atiku ba zai kai labari ba - Ali Modu

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

A baya, mun kawo labarin cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya yi tsokaci kan takarar da Atiku Abubakar zai yi ta neman kujerar shugaban kasa a babban 2027 da za a fafata a Najeriya.

Ali Modu Sheriff ya bayyana cewa Atiku Abubakar yana yin kidansa da rawarsa ne kawai shi kadai domin ba zai kai labari ba a zaben ganin cewa yanzu lokacin Kudu ne wajen ci gaba da mulkin kasar nan.

A cewarsa, shugabannin siyasar Najeriya sun cimma matsaya bayan yakin basasa domin tabbatar da daidaiton shiyyoyi a shugabancin kasar, wanda hakan zai ba wa kowane yanki damar jagorantar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng