Asirin Sanata Sirika Ya Bankada, an Jiyo Muryarsa da Aka Nada game da Badalaka
- Kotu ta ci gaba zama kan Sshari'ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika wanda ake zargi da badakala
- Shaidan EFCC ya tabbatar cewa muryar da ke cikin sakon ta Sirika ce, tana tattaunawa da Babban Sakataren ma'aikatar
- Kotu ta karbi takardun daskarar da wasu asusun banki, yayin da shaidar ta ce wasu takardun da aka gabatar ba su ambaci sunan Sirika ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shari'ar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ta dauki sabon salo a ranar Laraba, 8 ga Yulin 2026.
Mai Shari'a S.C. Oriji na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja ya saurari wani sakon murya da aka ce tsakanin Sirika da Babban Sakataren ma'aikatar, Enitan Abel.

Source: Facebook
An saurari muryar Sirika a kotu
Shaidar masu gabatar da kara ta 12 (PW12), Mataimakin Kwamandan EFCC, Christopher Odofin, ya tabbatar wa kotu cewa muryar da ke cikin sakon ta Sirika ce, cewar TVC News.
Odofin ya ce sakon muryar ya kunshi tattaunawa kan wata yarjejeniyar ba da shawarwari da ake takaddama a kanta tsakanin Sirika da Abel.
Ya kara da cewa Sirika ne ya aika da sakon muryar daga kasar Spain zuwa ga Enitan Abel.
Shaidar ta bayyana cewa mutumin da aka ambata a cikin sakon, wanda ya kusan shekara 70, shi ne Farfesa Gabriel Tilman, wanda aka bayyana a matsayin wakilin kamfanin Tinaero Nigeria Limited.
A cikin sakon, an ji Sirika yana cewa zai hada wani mutum da Tilman domin ya koya masa yadda ake gudanar da harkokin ba da shawara a Najeriya.
PW12 ya bayyana cewa mutumin da aka dora wa alhakin taimaka wa Tilman shi ne Yasir, wanda ya ce dan uwan tsohon ministan ne.
Haka kuma, shaidar ta ce sakon ya nuna Sirika yana bayyana Tilman a matsayin mutum da ya saba da ma'aikatar kuma babban abokinsa ne.
Odofin ya ce daga abin da Sirika ya fada a cikin sakon, ya fahimci cewa wasu ma'aikatan ma'aikatar ba sa son Tilman saboda yadda yake tilasta kansa a harkokin ma'aikatar.
Shaidar ta kuma bayyana cewa an yi wa kamfanin Tinaero rajista ne shekara guda kacal kafin a ba shi kwangiloli biyu, lamarin da EFCC ke ganin yana da muhimmanci a shari'ar.

Source: Facebook
Zarge-zargen da ake yi wa Sirika
Ana tuhumar Hadi Sirika tare da 'yarsa Fatima Hadi Sirika, surukinsa Hamma Jalal Sule da kuma kamfanin Al Buraq Global Investment mai alaka da 'yarsa.
Yayin tambayoyin da lauyan Sirika, Kanu Agabi (SAN), ya yi wa shaidar, Odofin ya ce wata takarda da aka gabatar a matsayin hujja neman takardar rashin adawa daga Hukumar BPP ce domin amfani da tsarin zababben bayar da kwangila.
Ya tabbatar cewa Babban Sakataren Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama, Enitan O. Abel, ne ya sanya hannu kan wannan takarda, cewar Premium Times.
Shaidar ta kuma bayyana cewa wata takarda daga BPP da aka gabatar a kotu martani ne ga bukatar ma'aikatar kan tsarin bayar da kwangilar.

Kara karanta wannan
'Dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta amince da kasafin N1.3bn don ma'aikatar bogi'
Sirika: Kotu ta yi watsi da hujjojin EFCC
A wani labarin, an ji cewa wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da muhimman hujjojin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Matakin ya biyo bayan ci gaba da shari’ar zargin damfarar kwangila N2.8bn da ake yi wa Hadi Sirika da wasu mutane.
Kotun ta ce bayanan da aka karɓo daga ‘yar Sirika da mijinta ba su cika sharuddan doka ba, saboda rashin bin tanadin doka.
Asali: Legit.ng

