Kwankwaso Ya Shiga Lamarin Tsare El Rufai da Barazanar Kashe Peter Obi
- Rabiu Musa Kwankwaso ya kare abokin gaminsa a jam’iyyar NDC da ya yi zargin akwai yiwuwar a nemi ganin bayan shi
- Idan har Peter Obi a yi wannan magana, tsohon gwamnan na Kano ya fada wa hukuma bai kamata a dauki abin da wasa ba
- Sanata Kwankwaso ya kuma yi kira da a yi adalci a shari’ar da gwamnatin tarayya ta ke yi da Malam Nasir El-Rufai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar NDC a zaben 2027 ya soki gwamnatin tarayya.
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tir da gwamnatin ne saboda zargin barazanar da Peter Obi ya yi da kuma yadda ake cigaba da tsare Nasir El-Rufai.

Source: Facebook
Rabiu Kwankwaso ya nema wa Peter Obi kariya
A wani jawabi da ya fitar a shafin X a yammacin Alhamis, ‘dan takaran na NDC ya ce akwai bukatar gwamnati ta ba Peter Obi kariya sosai.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya nuna yana cikin barazana har ta kai yana ganin ba dole ba ne a shirya zabe mai zuwa a badi yana da rai.
Obi ya shaida wa Chude Jideonwo cewa a matsayinsa na ‘dan adawa mai neman ganin bayan mulkin Bola Tinubu a 2027, kasuwancinsa ya tabu.
Tunda ‘dan takaran shugaban kasar ya fito ya nuna akwai yiwuwar ana son ganin bayan shi, Kwankwaso ya ce bai dace a dauki abin da wasa ba.
Dole a yi wa Nasir El-Rufai adalci - Kwankwaso
Baya ga batun Obi, Sanata Kwankwaso ya bukaci a yi adalci da gaskiya kamar yadda doka ta tanada a shari’o'in da ake yi da Nasir El-Rufai.
Jagoran na Kwankwasiyya ya nuna damuwarsa game da yadda El-Rufai yake a garkame har yau, musamman da ya ji maganganun wata matarsa.
Ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba, Malam El-Rufai ‘dan Najeriya ne kamar kowa da ya dace a bi ka’ida a lamarinsa kuma ana dauka yana da gaskiya har sai kotu mai iko ta same shi da laifi.
Ganin har yau tsohon gwamnan Kaduna bai samu ‘yanci ba, Kwankwaso ya ce an kakaba wasu ka’idojin beli ne da za su yi wahalar a iya cika su.
Sanata Kwankwaso ya ce:
Tunda ba a taba samun Malam El-Rufai da laifi a kotu ba, ya cancanci a yi masa shari’a ta adalci da gaggawa.
Bugu da kari, Punch ta rahoto babban ‘dan siyasar yana kira da a kula da lafiyar jagoran na ADC.
Wani kira da ‘dan takaran na mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC ya yi shi ne a guji amfani da karfin gwamnati wajen warware sabani na siyasa.
Ka da mu yi amfani da wannan domin magance sabanin siyasa. Idan ana so damukaradiyyarmu ta daure, dole kowan ‘dan kasa – karami ko babba, ba tare da la’akari da kabila, addini, ko mazhabar siyasarba, a dauke kamar kowa ta fuskar doka a Gwamnatin tarayyar da ta ke domin ba mu kariya gaba daya.
- Rabiu Kwankwaso
Ga maaganar Kwankwaso a dandalin Facebook:
El-Rufai: Peter Obi ya zubar da hawaye
Labari ya gabata cewa Peter Obi mai neman zama shugaban Najeriya a NDC ya yi wa matar Nasir El-Rufai kuka da ya ji jawabinta game da mijinsu.

Kara karanta wannan
2027: Martanin Kwankwaso ga Ali Modu Sheriff bayan ya ce su Obi ba za su kai labari ba
Mista Peter Obi ya zubar da hawaye da ya ji maganganun Asiya El-Rufai tana rokon Bola Tinubu ya saki tsohon gwamnan da yake tsare har gobe.
'Dan siyasar bai tare da Nasir El-Rufai a jam'iyyance amma ya fada wa gwamnatin Bola Tinubu cewa akwai bukatar a yi adalci a shari'ar da ake yi.
Asali: Legit.ng
