Mutanen Gari Sun Nuna Bajinta da 'Yan Bindiga Suka Farmaki Garuruwa a Katsina
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina
- Hatsabiban 'yan bindigan sun hallaka mutane tare da raunata wasu daban yayin hare-haren da suka kai da daddare
- Mutanen sun fito an yi arangama tsakaninsu da 'yan bindigan duk da cewa sun fi su karfin makaman yaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Aƙalla mutane uku ne aka kashe lokacin da miyagu da ake zargi 'yan bindiga ne suka ƙaddamar da hare-hare a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kuma raunata mutane a hare-haren wadanda suka kai kan garuruwa dama a yankin karamar hukumar Malumfashi a daren ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce majiyoyi sun bayyana cewa garuruwan da abin ya shafi sun haɗa da Gobirawa, Badole, Yammama, da kuma Dayi.
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Katsina
A cewar mazauna garin, hare-haren sun zo ne a matakai guda biyu, inda Gobirawa da Badole suka fi fuskantar tashe-tashen hankulan yayin da 'yan bindigar suka afka wa gidaje tare da buɗe wuta ba kakkautawa.
Wani mazaunin garin, Abdul’aziz Abdul’aziz, ya bayyana lamarin a matsayin wata damuwa ta rashin tsaro da kuma koma-baya bayan watanni da aka shafe ana samun kwanciyar hankali a sassan Malumfashi.
“Mun fara jin daɗin zaman lafiya, kuma mutane sun koma gonakansu. Farat ɗaya, sai ga 'yan bindigan sun sake kawo hare-hare."
- Abdul'aziz Abdul'aziz
Mutanen gari sun fafata da 'yan bindiga
Ya ƙara da cewa duk da haɗarin da ke akwai, mazauna garin sun haɗu domin tunkarar maharan.
“Abin da ya fi ba da mamaki shi ne ƙarfin zuciya da mutane suka nuna. Sun fuskanci maharan ba tare da tsoro ba, kodayake maharan sun fi su makamai."
- Abdul'aziz Abdul’aziz
An yabawa jami'an tsaro
Mazauna garin, sai dai kuma, sun yaba da saurin mayar da martani na jami'an tsaro, inda suka bayyana cewa tura ayarin jami'an 'yan sanda na sintiri a kan lokaci tare da 'yan banga ya taimaka wajen korar maharan da kuma hana ƙarin asarar rayuka.

Source: Original
A cewarsu, jami'an tsaron cikin hanzari sun shiga sassan da abin ya shafi, inda suka gudanar da sintiri na dare baki ɗaya kuma suka dawo da kwanciyar hankali.
Ƙoƙarin samun tabbaci a hukumance daga rundunar 'yan sanda ya ci tura, duba da cewa jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sandan jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, bai amsa kiran waya da sakonnin tes ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto.
'Yan bindiga sun kashe liman
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai harin da ya yi sanadiyyar hallaka wani limamin masallaci a jihar Sokoto.
Yan bindigan sun kuma yi garkuwa da mutane 12 a wani hari da suka kai ƙauyen Illelar Dawagware da ke yankin karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto.
Maharan, waɗanda aka ƙiyasta yawansu ya kai kusan mutane 30, an bayyana cewa sun shafe kusan mintuna 30 suna cin karensu ba babbaka.
Asali: Legit.ng

