Gagdi: Dan Majalisar APC Ya Nuna Yatsa ga 'Yan Adawa kan Rashin Tsaro
- Matsalar rashin tsaro na ci gaba da addabar sassa daban-daban na Najeriya duk da kokarin da gwamnati ta ce tana yi
- Dan majalisa na jam'iyyar APC, Yusuf Gagdi, ya soki halayyar da wasu 'yan adawa ke nunawa kan matsalar rashin tsaro
- Yusuf Gagdi ya bayyana cewa akwai ayar tambaya kan yadda matsalar ke kara ruruwa yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani mamba na Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi, ya yi zargi kan wasu bangarori na ‘yan adawa dangane da matsalar rashin tsaro.
Yusuf Gagdi ya zargi wasu 'yan adawa da amfani da kalubalen tsaron Najeriya domin cimma manufar siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam daga jihar Plateau, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026.
Me Gagdi ya ce kan rashin tsaro?
Ya bayyana cewa ko da yake rashin tsaro babban abin damuwa ne ga kasa, wasu ‘yan siyasa sun fi nuna sha’awar yin amfani da shi domin bata sunan gwamnatin tarayya maimakon bayar da mafita ta zahiri.
Da yake mayar da martani kan fargabar cewa tabarbarewar tsaro na iya kawo cikas ga damar sake zabar Shugaba Bola Tinubu da kuma makomar jam’iyyar APC a 2027, dan majalisar ya yi watsi da shawarar cewa mambobin jam'iyya mai mulki su kalli lamarin ta fuskar siyasa.
Ya nuna yatsa ga 'yan adawa
“Sun fada hannun ‘yan adawa, wadanda ke yin siyasa da rayukan ‘yan Najeriya. Zan fadi hakan ba tare da tsoron kowa ba. Idan har akwai wani daga jam’iyyata da ke tunanin cewa wannan shi ne zai rushe gwamnati mai ci yanzu, to hakan na nufin mutanen nan ba masu kishin kasa ba ne."
“Idan ka kalli yadda wadanda ke adawa da wannan gwamnati ke magana, zan iya gaya maka cewa ko da ba su ne ke rura wutar lamarin ba, suna farin ciki da shi, wasunsu, ba duka ba."
"Idan ka kalli kalaman wasu mutane da ya kamata su kasance shugabannin wannan kasa, lokacin da suke magana kan abubuwan da ‘yan Najeriya ke fuskanta, za ka ga kamar suna jin dadin halin da Najeriya ke ciki."
"Maimakon su yi kuka da kuma samar da mafita, sai su danganta shi da cewa gwamnati ta gaza wajen magance matsalar, domin kawai su cimma wata manufar siyasa."
- Yusuf Gadgi
Ya nuna ayar tambaya kan rashin tsaro
Dan majalisar ya tambayi dalilin da ya sa ake ganin rashin tsaron ya tsananta daidai lokacin da harkokin siyasa gabanin babban zabe mai zuwa ke kara ruruwa.
“Idan ka tambaye ni kafin zuwan wannan gwamnati, Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin gyara batun rashin tsaro, kuma a fahimtarka, ya gaza yin hakan. Amma ko zan iya tambayar me ya sa matsalar ke dada tsananta daidai lokacin da muke fuskantar lokacin yakin neman zabe?”
- Yusuf Gagdi

Source: Facebook
Yusuf Gadgi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance da hadin kai da kishin kasa, inda ya jaddada cewa ya kamata 'yan kasa su tsawatar wa gwamnati ba tare da mayar da tsaron kasa ya zama makamin siyasa ba.

Kara karanta wannan
Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa
Maganar Kwankwaso kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan rashin tsaro.
Rabiu Kwankwaso wanda shi ne madugun Kwankwasiyya, ya yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron Najeriya cikin gaggawa.
Ya yi magana yana mai gargadin cewa rashin tsaro na ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar duk da makudan kuɗi da ake kashewa a fannin.
Asali: Legit.ng

