Jirgin Sojojin Najeriya Ya Far Wa Yan Bindiga Kimamin 200, Ya Musu Gagarumar Illa a Neja
- Rahotanni sun ce hare-haren jiragen yaki na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta'adda da dama a Jihar Neja
- Dakarun sojojin sun yi luguden wuta ta sama ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin sama da 'yan ta'adda 200
- Bayan kashe da dama daga cikin yan bindigar, an kuma lalata wani wurin da ake zargin suna tara kayayyaki da man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Dakarun rundunar sojin sama da ke karkashin Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta'adda da dama a hare-haren sama da suka kai a karamar hukumar Mariga ta Jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun kai wadannan hare-haren ne bayan samun bayanan sirri masu inganci, wadanda ke nuna 'yan bindiga kimamin 200 na tafiya a kan babura.

Source: Twitter
Zagazola Makama, wadda ke dauko rahotannin yaki da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi, ya wallafa a shafin X cewa an gudanar da hare-haren ne a ranar 29 ga Yuni, tare da dakile yunkurin 'yan ta'addan a yankin.
Sojoji sun samu nasara a Neja
Rahoton ya ce an kaddamar da farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa sama da 'yan ta'adda 200 dauke da babura suna tafiya ta hanyar Sangeko zuwa Dogon Dawa da Womba.
An ce kungiyar na shirin kai hare-hare tare da karfafa sansanonin da take amfani da su a yankin dajin Kamuku.
An kashe 'yan ta'adda a kan babura
A cewar Makama, masani kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro, jirgin sojin sama ya gudanar da aikin leken asiri da sa ido (AISR), inda ya rika shawagi a yankunan Womba, Dogon Dawa, Kurugin, Birnin Gwari, Polewaya da Udawa.
Rahoton ya ce:

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
"A yayin aikin, matukan jirgin sun gano wasu 'yan ta'adda a kan babura da ke tafiya zuwa dajin Kamuku."
"Bayan tabbatar da wadanda ake bayani su ne, jirgin ya yi amfani da makamai wajen kai musu farmaki, lamarin da ya yi sanadin kashe su."
Rahoton ya kara da cewa bayan tantance barnar da aka yi tare da hadin gwiwar dakarun kasa, an tabbatar da kashe wadanda ake zargi da ta'addanci.
Jirgi ya sake murkushe yan bindiga
A wani farmaki daban da aka kai a wannan rana, jirgin ya sake gudanar da sintiri a yankunan Dogon Dawa, Kurugin Maidawa da sauran wuraren da ke makwabtaka.
A yayin sintirin ne aka hango wasu 'yan ta'adda masu yawa na tafiya suna tura babura a wani wuri da ake zargin suna tara kayayyaki da kuma cika tankin babura da man fetur.

Source: Twitter
Rahoton ya ce rundunar ta dauki wurin a matsayin muhimmiyar cibiyar samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda, sannan ta kai harin sama cikin tsari.
An ce harin ya lalata wurin tare da kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan, kamar yadda The Cable ta kawo.
Sojoji sun naƙasa yan ta'adda a Borno
A baya, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun ci gaba da kai hare- hare kan maboyar 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas.
Sojojin sun kashe tarin 'yan ta'adda, ciki har da manyan kwamandojin Boko Haram/ISWAP da dama a wani samame da suka kai a Borno.
Aikin, wanda sashen dakarun saman na rundunar Operation Hadin Kai ya gudanar, ya farmaki sansanonin 'yan ta'adda da ke Metele, wani sanannen wurin buya na 'yan tawaye a jihar Borno.
Asali: Legit.ng

