Yadda Al Jazeera Ta ba Hadimin Tinubu Hakuri a Asirce kan Wata Hira da Suka Yi
- Hadimin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da titsiye da wani babban ɗan jarida ya yi masa
- Daniel Bwala ya ce kafar Al Jazeera ta ba shi hakuri a asirce kan hirarsa da Mehdi Hasan, amma ta ki fitarwa a bainar jama'a
- Bwala ya ce an gyara hirar ta hanyar cire wasu muhimman sassa da suka nuna yana kalubalantar Hasan, lamarin da ya kira rashin da'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara, Daniel Bwala ya bayyana yadda babbar gidan jarida ta ba shi hakuri.
Bwala ya ce kafar yada labarai ta Al Jazeera ta ba shi hakuri a asirce kan hirarsa da Mehdi Hasan a shirin Head to Head.

Source: Twitter
Bwala ya bayyana haka ne yayin wata hira da Morayo Afolabi-Brown, wadda aka wallafa a YouTube, watanni bayan hirarsa da Al Jazeera a watan Maris na 2026.
Bukatar da Bwala ga Al Jazeera
Sai dai ya ce kafar ta ki amincewa da bukatarsa na fitar da wannan hakuri a bainar jama'a, abin da ya sa ya umurci lauyoyinsa da ke Ingila su shigar da kara.
A cikin hirar, Mehdi Hasan ya tambaye shi kan tsofaffin kalaman da ya taba yi yana sukar Shugaba Bola Tinubu lokacin da yake goyon bayan Atiku Abubakar.
Da aka tambaye shi ko ya bukaci Hasan ya ba shi hakuri bayan hirar, Bwala ya ce Al Jazeera ta amince da kuskurenta, amma ta ki bayyana hakan a fili.
Ya ce sun ba shi hakuri a asirce, amma suka ce ba za su wallafa hakan a shafukan sada zumunta ba saboda hakan zai iya shafar martabar kafar.
Bwala ya ce jigon hakurin shi ne cewa Al Jazeera ta kasa sanar da shi tun farko cewa za ta binciki amincinsa ta hanyar tambayoyi kan tsofaffin kalamansa.
Ya ce bisa ka'idojin aikin jarida, ya kamata su sanar da shi cewa batun zai kasance cikin hirar, kuma sun amince da cewa sun yi kuskure.

Source: Twitter
Zargin da Bwala ke yi a hirar
Bwala ya ce shirin ya dauki awa daya da mintuna 30, amma Al Jazeera ta fitar da mintuna 49 kacal, inda ta cire wasu muhimman sassa.
Ya zargi kafar da cire wuraren da yake gyara bayanan Hasan kuma masu sauraro suna tafa masa, tare da barin wuraren da Hasan yake samun tafi.
Har ila yau, ya ce Hasan ya rika nuna tsofaffin bidiyonsa ba tare da bayyana cikakken mahallin kalaman ba, lamarin da ya ce ya bata masa suna.
A cewarsa, bayan Al Jazeera ta ki yin afuwa a bainar jama'a, ya umurci lauyoyinsa a Ingila su shigar da kara, kuma har yanzu shari'ar tana gaban kotu.
Ya kara da cewa lauyoyinsa sun ba shi shawarar cewa abin da aka yi masa ya kai matsayin bata suna, saboda haka ya yanke shawarar neman hakkinsa a kotu.
Bwala ya yi wa Atiku shagube
An ji cewa Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce haɗakar jam’iyyun adawa da ake cewa ana yi kafin zaɓen 2027 ba za ta kai ko ina ba.
Ya ce manyan yan siyasa da jam'iyyu kamar su PDP da LP sun musanta shiga kowace irin tattaunawar haɗin gwiwa da Atiku Abubakar.
Bwala ya ce APC ce ke samun karuwa, tana karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyu, ba haɗakar adawa ba kamar yadda ake ikirari.
Asali: Legit.ng


