Tsaro: Najeriya na Neman Agajin Kasashe bayan Trump Ya Ce Ya Gama Kare Kiristoci

Tsaro: Najeriya na Neman Agajin Kasashe bayan Trump Ya Ce Ya Gama Kare Kiristoci

  • Gwamnatin Najeriya ta buƙaci ƙarin haɗin gwiwa da ƙasashen waje kan yaƙi da matsalar tsaro, tana mai cewa hakan na da matuƙar amfani
  • Ministan harkokin waje ya ce matsalar tsaro, harkokin siyasa da tattalin arziki da duniya ke fama da su sun ya zama wajibi kasashe su hada kai
  • Jami'an kwalejin tsaro Najeriya sun ce musayar al'adu na taimakawa wajen ƙarfafa alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe a yaki da rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran ƙasashe wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Gwamnatin ta bayyana cewa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa na da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa a duniya.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi magana kan kashe malamar Islamiyya a Kaduna

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na bayani a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa karamin ministan harkokin waje, Ambasada Sola Enikanolaiye, ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar al'adu da abinci ta kasa a Abuja a ƙarshen mako.

Tsaro: Najeriya ta nemi agaji

Ta bakin Ambasada Bukar Kalambe, wanda ya wakilce shi, karamin ministan ya ce duniya na ƙara fuskantar barazana sakamakon matsalolin tsaro, siyasa da tattalin arziki, wanda hakan ya sa haɗin kai ya zama mafi muhimmanci fiye da kowane lokaci.

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron Amurka ke ci gaba da kasancewa a Najeriya, da kuma ikirarin Donald Trump na cewa ya kare Kiristocin kasar daga hare-hare.

Enikanolaiye ya ce halartar ɗalibai daga ƙasashen waje na nuna amincewar ƙasashen da kulla alaka da kwalejin tsaro ta kasa, tare da ƙarfafa rawar da take takawa wajen bunƙasa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

“Yawancin abokantakar da ake ƙullawa a cikin kwalejin na ci gaba har bayan kammala karatu, kuma sau da yawa suna zama muhimman hanyoyin haɗin gwiwar diflomasiyya, soja da dabarun tsaro tsakanin ƙasashe,”

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 game da dokar yan sandan jihohi ta Najeriya

In ji shi.

Ministocin harkokin wajen Najeriya
Sola Enikanolaiye da Bianca Ojukwu a Abuja. Hoto: Imran Muhammad
Source: Facebook

Dalilin tsara taro a Abuja

Kwamandan kwalejin tsaro ta kasa, Rear Admiral Abdullahi Ahmed, ya ce an tsara shirin ne domin gina haɗin gwiwar dabarun tsaro ta hanyar musayar al'adu.

Trust Radio ya rahoto ya ce fahimtar al'adun juna, abinci, kiɗa da al'adu na ƙarfafa dangantaka tare da inganta haɗin gwiwa wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ƙasashe ke fuskanta tare.

Wakilin kungiyar jakadun kasashen waje, Isaac Parashina, ya ce taron ya bai wa mahalarta damar ƙarfafa dangantaka da ke zama ginshiƙin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe, baya ga horon ƙwarewa da shugabanci da suke samu.

Sojoji su bindige 'yan ta'adda

A wani labarin, mun rahoto muku cewa sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da wasu da ake zargi 'yan ta'adda ne a wani yanki na jihar Benue.

Dakarun Najeriya sun samu kiran gaggawa ne kan cewa wasu mutane dauke da makamai sun yi yunkurin kai hari wata kasuwar doya.

Biyo bayan samun labarin, dakarun sun nufi wajen tare da fara musayar wuta da wadanda ake zargin, lamarin da ya jawo kashe wasu mahara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng