Da Gaske Dan Karamin Yaro ne Ya Sace Janar Rabe a Katsina? Gaskiya Ta Fito
- Wasu mutane sun yi ta yada cewa wai wani karamin yaro ne ya sace Janar Rabe Abubakar mai ritaya a Katsina
- Sai dai wani bincike ya gano gaskiya tare da yin karin haske kan bayyanar yaron a wani hoto da aka yada cewa shi ne ya sace shi
- Binciken ya gano cewa kafafen yada labarai da hukumomin tsaro ba su taba bayyana yaron a matsayin wanda ake zargi da hannu a satar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - An yi ta yada wasu rahotanni game da sace Janar Rabe Abubakar mai ritaya a jihar Katsina kafin rasuwarsa a hannun yan bindiga.
An sace Janar Rabe ne da matarsa a ranar 30 ga Mayu 2026 a kan hanyar Marabar Musawa–Kafinsoli a Jihar Katsina a lokacin harin ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan
Harin Borno: Adadin daliban da ake nema yanzu ya haura 30, wani kansila ya yi bayani

Source: Facebook
Bincike ya karyata ikirarin da wani shafin Facebook mai suna Spynigeria.NG ya wallafa, wanda ke cewa yaron da ya bayyana a wani hoto shi ne ya sace tsohon sojan.
Binciken da aka yi kan sace Rabe
A binciken Dubawa, an gano cewa babu isasshiyar hujja da ke tabbatar da wannan ikirari da ake ya yadawa.
Ko da yake an yada hoton tare da rahotanni kan satar Janar Rabe, babu wata shaida daga hukumomin tsaro ko kafafen yada labarai masu inganci da ta tabbatar da hakan.
Rahotannin Premium Times, Daily Trust da Punch sun tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da masu garkuwar suka fitar da bidiyo suna nuna Janar Rabe da matarsa suna rokon a taimaka musu.

Source: Facebook
Gaskiyar rahoton hoton yaro a sace Janar Rabe
Majiyoyi suka ce wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga mai suna Kachalla Muhammadu yana da alaka da lamarin, kuma ya tuntubi iyalan wadanda aka sace domin tattaunawa.
Sai dai duk da yawan rahotannin da aka wallafa, binciken ya gano babu wata hukuma ko kafar yada labarai mai sahihanci da ta bayyana yaron da ke cikin hoton a matsayin daya daga cikin masu garkuwar.
Masu binciken sun kuma tuntubi Mai kula da Yada Labarai na Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Edward Onoja, domin karin bayani, amma ya ki yin tsokaci kan lamarin.
Binciken hoton ta hanyar 'reverse image search' ya nuna cewa hoton ya rika yawo ne tare da bidiyon da masu garkuwar suka saki bayan sace Janar Rabe da matarsa.
An gano cewa an yada hoton a kafofin sadarwa, suna zargin yaron yana cikin wadanda suka wallafa bidiyon a TikTok kuma suna alakanta shi da kungiyar Kachalla Muhammadu.
Sai dai an ce wadannan ikirarai, babu wata hujja da ta tabbatar cewa yaron ya shiga satar Janar Rabe ko kuma yana cikin wadanda suka aikata wannan laifi.
Sojoji sun ceto matar janar Rabe
An ji cewa Dakarun Operation Fansan Yanma sun ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar bayan wani farmaki da suka kai jihar Katsina.
Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun harbi matar kafin su tsere lokacin da sojoji suka kai masu farmakin a kauyen Tunga.
Rundunar sojojin Najeriya dai ta ce ana ci gaba da farautar ‘yan bindigar karkashin Operation Clean Sweep III a yankin Matazu.
Asali: Legit.ng
