Adeboye: 'Abin da Ubangiji Ya Gaya Mini kan Dalibai da Malaman da Aka Sace a Oyo'
- Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya yi tsokaci kan daliban da aka sace a jihar Oyo
- Fasto Adeboye ya bayyana cewa Ubangiji ya yi masa magana dangane da daliban wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su
- Malamin addinin na Kirista ya bayyana Ubangiji ya sanar da shi abubuwa da dama da ke faruwa a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya yi magana kan daliban da aka sace a jihar Oyo.
Fasto Adeboye ya bayyana abin da ya ce ubangiji ya faɗa masa game da ɗalibai da malaman da aka sace daga jihar Oyo.

Source: Instagram
Fasto Adeboye ya bayyana hakan ne a wurin taron karramawa na "US-Nigeria Faith Heroes Award Gala" wanda ƙungiyar Save Nigeria Group ta shirya a birnin Washington ranar 23 ga watan Yunin 2026, rahoton Premium Times ya nuna hakan.

Kara karanta wannan
El Rufa'i: Dalilin kotu na ci gaba da fatali da bukatar belin tsohon gwamnan Kaduna
Me Adeboye ya ce kan sace daliban Oyo?
Fasto Adeboye ya ce ya nemi jagorancin ubangiji ba tare da bata lokaci ba bayan sace daliban. Dattijon mai shekaru 84 ya ce:
"Na tsinci kaina cikin halin kuka ga ubangiji domin mun kasance muna azumi da addu'a saboda wani rukunin dalibai da aka sace."
"Masu garkuwar sun ji cewa gwamnati ba ta mayar da martani da sauri ba wajen ba su kuɗaɗen da suka nema, sai suka yanka malaminsu kuma suka nuna bidiyon ga sauran duniya."
“Daga nan wasu mutane suka fara magana, suna ƙalubalantar mu da muka ce muna addu'a. Suka ce, ‘Kuna azumi, kuna addu'a, ina Allahn na ku yake?’"
"Don haka sai na je gaban Ubangiji cikin addu'a, da tsananin baƙin ciki. Na ce, ‘Ubangiji, ka ji su. Sun ce, ‘Ina Allahnmu yake?’ Sai kuwa Ubangiji ya yi magana da ni. Ya faɗa mini cewa sakin yaran zai kasance mai cike da ban mamaki.”

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu
Me Ubangiji ya gayawa Fasto Adeboye?
Bugu da ƙari, malamin addinin ya bayyana cewa Ubangiji ya yi masa alƙawarin zai sake ba shi amsa game da shirin sakin ɗalibai da malaman da aka sace.
Ya kuma bayyana cewa Ubangiji ya yi masa magana a kan wasu batutuwa da dama da suka shafi ƙasar, TheCable ta kawo labarin.
“Ubangiji bai faɗa mini lokaci ko cikakken bayani ba. Daga nan sai ya ce mini na bar hakan a hannunsa, sannan ya ce zai yi magana da ni game da abin da zai faru bayan wannan lamari."
“Wasu daga cikin abubuwan da ya faɗa, ya ambaci abin da zai faru da waɗanda suke ɗaukar nauyin ta'addanci da garkuwa da mutane a Najeriya. Ya kuma yi magana a kan wasu abubuwa da dama. Ba ni da masaniyar abin da zai faru a nan."
- Fasto Enoch Adeboye

Source: Facebook
Fasto Adeboye ya kare Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Fasto Enoch Adeboye da ke shugabantar cocin RCCG, ya kare Shugaba Bola Tinubu daga sukan da ake masa game da ta'azzarar rashin tsaro.

Kara karanta wannan
Adeboye: Malamin addini ya kare Tinubu kan rashin tsaro, ya ba shi shawara kan hafsoshi
Fasto Adeboye ya bayyana cewa shugaban kasar ya cika nauyin da ke kansa ta hanyar bayar da umarni ga dakarun sojoji.
A cewarsa, ya ba wa shugaban ƙasar shawarar ya ba wa hafsoshin tsaro wa'adin kwanaki 90 domin su murƙushe ta'addanci ko kuma su yi murabus.
Asali: Legit.ng