Asiri Ya Tonu: Sojoji Sun Rike Masu Kera Makamai ga 'Yan Ta'addan Arewa ta Yamma

Asiri Ya Tonu: Sojoji Sun Rike Masu Kera Makamai ga 'Yan Ta'addan Arewa ta Yamma

  • Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun tarwatsa wata haramtacciyar cibiyar ƙera makamai a wani yanki na jihar Kebbi
  • Yayin da aka kai farmaki masana'anatar, sojoji sun ƙwato bindigogi biyar da aka ƙera a cikin gida masu kama da AK-47 tare da kama mutum biyu
  • Jami'an tsaro sun fara ƙarin bincike da samame domin cafke sauran waɗanda ke da hannu a cibiyar da kuma dakile safarar makamai a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Sojojin Operation Fansnan Yamma sun tarwatsa wata ƙungiyar da ake zargi da ƙera makamai ba bisa ƙa'ida ba a jihar Kebbi.

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun ƙwato bindigogi biyar da aka ƙera a cikin gida yayin samamen da aka gudanar bisa bayanan sirri da suka samu.

Kara karanta wannan

Ambaliya ta mamaye yankunan Legas, hanyoyi sun yi makil, lantarki ta katse

Wadanda aka kama a Kebbi
Mutane 2 da sojoji suka kama a jihar Kebbi. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da farmakin da sojojin suka kai ne a wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

Wajen da ake kera makamai a Kebbi

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an kai samame wani keɓaɓɓen wuri da ake zargin ana amfani da shi wajen ƙerawa da rarraba makaman da aka yi a cikin gida ga ƙungiyoyin ta'addanci da 'yan bindiga da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma.

A cewar majiyoyin, sojojin sun kai farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka binciki wurin sosai tare da ƙwato bindigogi biyar masu kama da AK-47 da aka ƙera a cikin gida.

An kuma kama mutane biyu da ake zargi mambobin ƙungiyar ne, waɗanda ake kyautata zaton suna da hannu wajen ƙerawa da rarraba makaman ba bisa ƙa'ida ba.

Majiyoyin sun bayyana cewa an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, abin da ke nuna ƙara ƙarfi a haɗin kan jami'an tsaro wajen yaƙi da ta'addanci da 'yan bindiga a yankin.

Kara karanta wannan

Akwai dalili: Gwamnatin tarayya za ta rushe tsarin karatun sakandare na JSS da SSS

Taswirar jihar Kebbi
Taswirar jihar Kebbi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An yi wa 'yan ta'adda illa

Sojoji sun ƙara da cewa wannan nasara babbar illa ce ga hanyoyin da masu laifi ke amfani da su wajen samar da makaman da ake ƙerawa a cikin gida ga ƙungiyoyin 'yan ta'adda.

Sojojin sun sanar da cewa dakile safarar makamai ba bisa ƙa'ida ba na daga cikin manyan manufofin Operation Fansan Yamma.

Mutanen da aka kama na ci gaba da kasancewa a hannun jami'an tsaro domin yi masu tambayoyi, da nufin gano sauran mambobin ƙungiyar, masu ɗaukar nauyin ayyukansu da kuma hanyoyin rarraba makaman.

Hukumomin tsaro sun kuma fara ƙarin samame domin cafke sauran waɗanda suka tsere da kuma rusa sauran sassan cibiyar ƙera makaman.

'Yan kwallo sun rasu a Kebbi

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kebbi ta sanar da cewa wasu 'yan kwallo 'yan asalin jihar sun rasu bayan sun yi hadarin mota.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar ya taimakawa wajen ceto mutanen da suka yi hadarin yayin da ya ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama.

Daga baya gwamnatin Kebbi ta tura tawaga ta musamman domin tallafawa iyalan 'yan kwallon da suka rasu da wadanda suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng