Adeboye: Malamin Addini Ya Kare Tinubu kan Rashin Tsaro, Ya Ba Shi Shawara kan Hafsoshi

Adeboye: Malamin Addini Ya Kare Tinubu kan Rashin Tsaro, Ya Ba Shi Shawara kan Hafsoshi

  • Shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama a ita a sassa daban-daban na Najeriya
  • Fasto Adeboye ya bayyana cewa masu sukar shugaban kasar kan rashin tsaro ba su fahimci yadda al'amura suke ba
  • Ya bayyana cewa ya ba Shugaba Bola Tinubu shawarar ya ba hafsoshin tsaro wa'adi domin kawo karshen matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington Amurka - Babban jagoran cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya kare Shugaba Bola Tinubu daga sukan da ake masa game da ta'azzarar rashin tsaro.

Fasto Adeboye ya bayyana cewa shugaban kasae ya cika nauyin da ke kansa ta hanyar bayar da umarni ga dakarun sojoji.

Adeboye ya kare Tinubu kan rashin tsaro
Fasto Enoch Adeboye da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Pastor E.A. Adeboye, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin taron karramawa na "US-Nigeria Faith Heroes Award Gala" wanda ƙungiyar Save Nigeria Group ta shirya a birnin Washington ranar 23 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

'Na taya uwata sayar da kosai': Hadimin Tinubu ya kare kalaman Oluremi

Adeboye ya kare Shugaba Tinubu

Adeboye ya ce waɗanda ke ɗorawa Tinubu laifin matsalolin tsaro na ƙasar ba su yi adalci ba ga rawar da shugaban ke takawa a matsayin babban kwamandan dakarun ƙasa.

“Ina buƙatar na bayyana wannan. Ba na goyon bayan waɗanda ke zargin shugaban ƙasa da rashin yin abin da ya dace. Idan babban kwamandan dakarun ƙasa ya ba wa na ƙasa da shi umarni, ya riga ya sauke nauyin da ke kansa. Ka da ku yi tsammanin zai je ya sa kayan sojoji ya je fagen daga."

- Fasto Enoch Adeboye

Ya ba da misali da Shugaba Trump

Yayin da yake kwatanta lamarin da na ƙasar Amurka, ya ƙara da cewa:

“Idan abokina Trump ya ba da umarnin a je a kai harin bam a kowane wuri, ba ya barin Fadar White House. Ya riga ya sauke nauyin sa. 'Na ba da umarni a nan, ku jefa bam a Iran', sannan sai ya wuce ɗakin barcinsa ya yi barci. Sauran abun kuma an bar wa masu aiwatarwa ne.”

Kara karanta wannan

APC na shirin sauya dan takararta na gwamna a Adamawa? Jam'iyyar ta yi bayani

Duk da kare shugaban ƙasar da ya yi, Adeboye ya amince cewa rashin tsaron ya ta'azzara kuma ya bazu zuwa sassan kudancin Najeriya, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Wace shawara ya ba Shugaba Tinubu?

Malamin addinin ya bayyana cewa ya tattauna batun tsaron ƙasar da Shugaba Tinubu da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, inda ya buƙaci shugaban ƙasar da ya ba da umarni mai ƙarfi ga shugabannin tsaron ƙasar.

A cewarsa, ya ba wa shugaban ƙasar shawarar ya ba wa hafsoshin tsaro wa'adin kwanaki 90 domin su murƙushe ta'addanci ko kuma su yi murabus.

“Na gaya masa cewa ya faɗa wa daukacin samarin soji, na rundunar ƙasa, ta ruwa da ta sama: ‘Kuna da kwanaki 90. Ku goge wannan shirme ko ku yi murabus.’ Sannan kuma a magane masu taimaka masu, wato masu ɗaukar nauyinsu."

- Fasto Enoch Adeboye

Fasto Adeboye ya kare Shugaba Bola Tinubu
Fasto Enoch Adeboye yana wa'azi a coci Hoto: Pastor E.A. Adeboye
Source: Facebook

Adeboye ya bayyana masu ɗaukar nauyin ta'addancin a matsayin mutane masu tasiri da kuɗi, ciki har da 'yan siyasa da 'yan kasuwa, inda ya nuna cewa tunkararsu tana da muhimmanci sosai ga kawo ƙarshen tasirin tashe-tashen hankula.

Kara karanta wannan

Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa

'Yan ta'adda sun sace dalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'adda sun kai farmaki a wata makarantar sakandaren gwamnati da ke jihar Borno.

Hatsabiban 'yan ta'addan sun yi awon gaba da daliban da ke rubuta jarabawar karshe ta NECO, tare da kashe wani malami yayin harin.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa an tura jami'an tsaro domin ceto su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng