An Bankado Wurare Masu Hadari a Abuja, an Kama Mutum 560 da Bindigogi

An Bankado Wurare Masu Hadari a Abuja, an Kama Mutum 560 da Bindigogi

  • Rundunar 'yan sanda ta FCT Abuja ta kaddamar da farmaki a wuraren da ake aikata laifuffuka daban-daban a cikin mako guda
  • Farmakin ya yi nasarar kama mutum 560 da kuma kwace bindigogi, alburusai da miyagun kwayoyi a hannun masu laifi
  • Kwamishinan 'yan sandan FCT, Ahmed Sanusi ya yi gargadin cewa za a ci gaba da kai irin farmaki har sai an tsabtace Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan Abuja ta sanar da cewa ta gano wurare masu haɗarin da dama a birnin tarayya, tare da kama mutum 560 a lokacin da ta kai farmaki a wuraren.

Kwamishinan 'yan sandan FCT, Ahmed Sanusi ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin taron manema labarai da aka yi a hedkwatar rundunar.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

Yan sanda a Abuja na bakin aiki
Yadda 'yan sanda suka kai farmaki a Abuja a kwanakin baya. Hoto: FCT Abuja Police Command
Source: Facebook

Punch ta bayyana cewa an kai farmakin ne bayan samun bayanan leƙen asiri da hadin gwiwar al'ummar yankunan da 'yan sanda.

Yadda aka kai farmaki a Abuja

Jami'an 'yan sanda daban-daban na rundunar FCT ne suka rabu gida biyu suka gudanar da farmaki a lokaci ɗaya, wanda ya kai ga kamun mutum 560.

Baya ga kama mutanen, a lokacin ayyukan an kwace bindiga kirar gida guda ɗaya, da kuma wata bindigar AK-47 ta gida, tare da alburusai uku.

Daily Post ta rahoto cewa an kuma kwace miyagun ƙwayoyi iri daban-daban da sauran abubuwan da ake zargi ana amfani da su wajen aikata laifuffuka a samamen da aka kai..

Karin bayani daga 'yan sanda

CP Sanusi ya ƙara da cewa a lokacin da aka kai farmaki a ƙaramar hukumar Kwali, Abaji da Kuje, an kama mutane huɗu da ake zargi da harkar sace mutane da kuma wadanda ake tuhuma da samar da alburusai da miyagun ƙwayoyi ga 'an fashi.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke mahaifin wanda ya kafa ma'aikatar bogi a gwamnatin Tinubu

Kwamishinan ya ce:

"Nasarorin da muke gabatarwa a yau sun nuna tsayuwar rundunar 'yan sanda ta FCT wajen tabbatar da cewa aikata laifuffuka ba zai bunƙasa a cikin babban birnin tarayya ba."
Tunji Disu a office a Abuja
Sufeton 'yan sandan Najeriya, Tunji Disu. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan sanda na cigaba da aiki

Ahmed Sanusi ya ƙarfafa cewa hukumar ba za ta yi wasa ba saboda nasarar da aka samu har sai an kakkaɓe dukkan 'yan ta'adda a Abuja.

Yayin da ya ke cigaba da kira ga jama'a, CP Sanusi ya bukaci mazauna birnin da su ci gaba da ba rundunar bayanan da za su taimaka wajen magance aikata laifuffuka.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce yin hadin gwiwa tsakanin al'umma da 'yan sanda shi ne ginshiƙin tsaro a babban birnin kasar da ma sauran yankunan Najeriya.

Sojoji sun shirya kai farmaki

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta shirya kai farmaki kan duk wasu masu barazana ga kasar nan a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Akwai dalili': Rundunar 'yan sanda ta kama motocin mutane fiye da 80 a Kano

Yayin da ya yi bayani ga dakatu da 'yan Najeriya, Hafsun sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shuaibu ne ya bayyana cewa za su kara kaimi a taron Ranar Sojoji ta 2026 a jihar Rivers.

Laftanar Janar Waidi Shuaibu ya sanar da cewa suna sane da wasu 'yan ta'adda da ke shirin zama barazana a iyakokin Najeriya kuma za su dandana kudarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng