Farashin Mai Ya Haura Dala 80 bayan Trump Ya Sake Rura Rikicin Iran

Farashin Mai Ya Haura Dala 80 bayan Trump Ya Sake Rura Rikicin Iran

  • Kalaman shugaban Amurka, Donald Trump da sabon harin da ya kai Iran ya fara girgiza kasuwar man fetur da duniya da karin farashin 'danyen mai
  • Shugaba Donald Trump ya ayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da Iran ta rushe kuma babu wani dalili na ci gaba da batun sulhu
  • Masana na fargabar tashin farashin man fetur a Najeriya idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ƙara tsananta yayin da ake jin karin hare-haren da Amurka ke kai wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States – Farashin 'danyen mai a kasuwannin duniya ya sake yin tashin gwauron zabo, inda ya haura Dala 80 kan kowace ganga.

Wannan ya biyo bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da aka cimma da Iran ta zama tarihi.

Kara karanta wannan

Dangote ya zabi kasar da zai kafa sabuwar matatar mai a Afrika

Rikicin Iran da Amurka da ya dawo sabo ya fara rikita kasuwar mai
Shugaban Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi (dama) Hoto: Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

The Guardian ta wallafa cewa bayanan kasuwar mai sun nuna cewa farashin ɗanyen mai ya fara hawa daga Dala 72 zuwa dala 7 a ranar Talata,7 ga watan Yuli, 2026.

Farashin mai ya karu bayan kalaman Trump

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa daga baya kuma farashin 'dayen mai ya kai Dala 80 a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2026.

Trump ya bayyana yarjejeniyar fahimtar juna da Iran a matsayin wadda ba ta da wani amfani, bayan da Iran ta kai hare-hare kan jiragen ruwa da ke bi ta Hormuz, lamarin da ya sake ɗaga hankulan kasuwannin makamashi na duniya.

Rahotanni sun ce Iran ta kai hari kan jiragen kasuwanci uku da ke ratsa mashigar Hormuz a ranar Talata, 7 ga watan Yuli abin da ya jawo martanin sojojin Amurka.

An ce wani jirgin dakon iskar LNG ya kama da wuta bayan an kai masa hari, yayin da wani babban jirgin dakon mai na Saudiyya ya samu matsala a gabar tekun Oman.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca kaca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Sojojin Amurka sun kai hari

A martaninta, rundunar sojin Amurka ta kai hare-hare ta sama kan sama da wuraren soji 80 a cikin Iran. Hare-haren sun shafi yankuna da dama na bakin teku, ciki har da tsibirin Qeshm, Sirik da kuma babban tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas.

Bayan haka, gwamnatin Trump ta soke rangwamen takunkumin da ya bai wa Iran damar sayar da mai da kayayyakin man fetur, matakin da ake ganin zai rage wa Tehran wata muhimmiyar hanyar samun kuɗin shiga.

Ana tsoron rikicin zai shafi farashin jigilar mai ta Hormuz
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi a Florida. Hoto: Roberto Schmidt/Getty Images
Source: Getty Images

A gefe guda kuma, hedkwatar Khatam al-Anbiya ta Iran ta sanar da rufe mashigar Hormuz tare da yin gargaɗin cewa duk wani jirgin kasuwanci da zai yi yunƙurin wucewa zai iya fuskantar matakin soja kai tsaye.

Masana sun ce sabon rikicin ya rusa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Yuni, yayin da masu jiragen ruwa suka fara ƙara kuɗin jigilar mai saboda haɗarin da ke yankin kuma hakan zai iya shafar farashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

Amurka ta yi wa Iran barna

A baya mun wallafa labarin cewa rahotanni sun ce sojojin Iran takwas sun mutu a sababbin hare-haren da Amurka ta kai kudancin ƙasar Musulunci ranar Laraba 8 ga watan Yuli, 2026 bayyan sake ballewar rikici.

Amurka dai ta sake kai hare-hare kasar Iran yayin da ake ci gaba da tattaunawa bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya saboda wani hari da ta ce an kai kan jirgin da ke wuce wa ta mashigar Hormuz.

Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma ta tabbatar da cewa a shirye take ta maida martani a lokacin da aka tabbatar da cewa sulhun da aka shafe watanni ana kokarin cimma wa ya rushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng