Jihar Edo
A ranar juma’a, 13 ga watan Disamba ne yayan jam’iyyar APC suka gudanar da wani gangamin siyasa a garin Bini na jahar Edo inda aka samu hatsaniya da yayi sanadiyyar jikkata kananan yara guda biyu.
Kusan Dala Biliyan 1.35 Najeriya ta rasa a cikin farkon shekara bayan da aka ji cewa Najeriya ta na tafka asarar daruruwan Biliyoyi duk shekara. Yanzu haka a bana an sace gangar mai fiye da miliyan 22.
An kama su ne yayin atisaye na hikima da jami'an rundunar tsaron farin kaya na jihar Edo suka shirya musamman saboda masu laifin. An kama Amos a Ubiaja da ke karamar hukumar Esan ta kudu, yayin daka kama Kelvin mai shekaru 18
Majiyar Legit.ng ta ruwaito matar mai suna Eniobong Isonguyo ta hada baki ne da Faston cocin da suke zuwa tare da mijinta, mai suna Udoka Ukachukwu, inda take bashi dama yana saduwa da ita, har ta kai ga ya dirka mata ciki.
An samu gawar wani malamin jami'a mai suna Patrick Okojie, wanda ke koyarwa a wata jami'a dake karamar hukumar Auchi cikin jihar Edo, an samu gawar tashi ne bayan kwanaki hudu da bacewar shi...
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya mika makullan gidan ne ga Malama Noragbon Osaru a ranar Alhamis, 31 ga watan Janairu yayin daya kai ziyara jahar Edo inda ya kaddamar da sabbin rukunin gidaje guda 100 da gwamnatin jahar ta
APC tayi kamu a Jihar Edo bayan wani Jigon PDP ya canza sheka, Wani babban ‘Dan siyasan Jihar ne ya tsere daga PDP. Kenan Buhari ya kara samun kwarin-gwiwa bayan an yi wa tsofaffin ‘Yan PDP wanka da ruwan APC a Kudancin Najeriya.
Rundunar Yansandan jahar Edo ta sanar da cafke wani karamin yaro dan shekara goma sha shida mai suna Zakaria Chiahemba akan zarginsa da halaka uwardakinsa mai suna Rejoice Odogwu mai shekaru hamsin da uku a rayuwa.
Shi kuwa mutum ba uku ya faru ne mahadar titi ta Alohan, yayin da wasu yan bindiga dake tafe a cikin mota suka bude masa wuta a daidai lokacin da yake tafiya a kasa, kamar yadda wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyarmu.
Jihar Edo
Samu kari