ASUU Ta Koka kan Rashin Cika Alkawari, Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki a Jami'o'i 11 a Najeriya
- Kungiyar ASUU ta soki gwamnatocin jihohi akalla bakwai kan rashin cika yarjejeniyar da aka cimmawa tsakaninta da gwamnatin tarayya a 2025
- ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki a jami'o'i 11 da ke wadannan jihohi matukar aka gaza biyan haƙƙokin malamai daga nan zuwa karshen watan Yuli
- Ta yi kira ga gwamnonin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar tare da biyan dukkan basussukan da ake bin su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta yi barazanar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a jami'o'in jihohi 11 idan a ba a biya masu bukatunsu ba.
ASUU ta ce idan gwamnatocin jihohin Edo, Delta, Ondo, Adamawa, Borno, Taraba da Yobe ba su aiwatar da yarjejeniyar 2025 kafin karshen watan Yuli ba, za ta tsunduma yajin aiki.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ASUU ta reshen Benin da reshen Yola ne suka bayyana hakan a tarukan manema labarai daban-daban da suka gudanar ranar Litinin.
Sun zargi gwamnatocin jihohin da rashin aiwatar da yarjejeniyar duk da cewa watanni shida sun shude tun bayan rattaba hannu a kanta.
ASUU ta fara shirin rufe jami'o'i 11
Shugaban ASUU na shiyyar Benin, Farfesa Monday Igbafen, ya ce rassan ASUU da ke jami'o'in da abin ya shafa sun fara shirya mambobinsu domin tsunduma cikin yajin aikin sai baba-ta-gani.
Jami'o'in da abin ya shafa sun hada da:
1. Jami'ar Ambrose Alli da ke Ekpoma, jihar Edo
2. Jami'ar Adekunle Ajasin da ke Akungba-Akoko, jihar Ondo
3. Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Olusegun Agagu, Okitipupa, jihar Ondo
4. Jami'ar jihar Delta da ke Abraka
5. Jami'ar Delta da ke garin Agbor
6. Jami'ar Dennis Osadebay da ke Asaba, jihar Delta
7. Southern Delta University, Ozoro

Kara karanta wannan
El Rufa'i: Dalilin kotu na ci gaba da fatali da bukatar belin tsohon gwamnan Kaduna
8. Jami'ar jihar Adamawa da ke Mubi
9. Jami'ar jihar Borno da ke Maiduguri
10. Jami'ar jihar Taraba da ke Jalingo
11. Jami'ar jihar Yobe da ke Damaturu
Dalilin barazanar kungiyar ASUU
Igbafen ya bayyana cewa yayin da jami'o'in gwamnatin tarayya da wasu jami'o'in jihohi suka aiwatar da yarjejeniyar, jihohin da abin ya shafa har yanzu ba su biya CATA da sauran alawus-alawus da aka amince da su ba.
A nasa bangaren, mai kula da ASUU a shiyyar Yola, Dani Mamman, ya ce ci gaba da kin aiwatar da yarjejeniyar da kuma biyan sauran hakkokin malamai ya jefa jami'o'in cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali, in ji Daily Post.

Source: UGC
Ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci da kuma karya ka'idojin tattaunawar ma'aikata da gwamnati, yana mai cewa malamai ba sa neman wani abu da ya wuce hakkokinsu na doka.
ASUU ta yi kira ga gwamnonin jihohin da abin ya shafa da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar tare da biyan dukkan basussukan da ake bin su domin kauce wa shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
ASUU ta cimma matsaya da gwamnati
A baya, kun ji cewa ƙungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 bayan doguwar tattaunawa.
ASUU ta ce sabuwar yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga 1, Janairu, 2026, kuma an tsara sake duba ta a duk bayan shekaru uku.
Yarjejeniyar ta mayar da hankali sosai kan walwalar malaman jami’o’i, inda aka amince da karin albashi kashi 40 cikin 100 ga dukkan ma’aikata masu koyarwa.
Asali: Legit.ng

