Abubuwan Fashewa Sun Tashi da Sojan Isra'ila a Lebanon
- Wani sojan kasar Isra'ila ya jikkata sosai sakamakon wasu abubuwan fashewa da suka tashi da shi a Kudancin Lebanon
- Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Lebanon sun ce an kai hari ta sama a Kudancin ƙasar duk da yarjejeniyar da aka cimma
- A daya bangaren, kwamandan CENTCOM na Amurka ya gana da shugabannin Lebanon da Isra'ila kan lamuran tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lebanon - Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta sanar da cewa wani sojan ta ya jikkata ƙwarai sakamakon wata fashewa da ta auku a Kudancin Lebanon.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da takaddama kan ficewar sojojin Isra'ila daga Lebanon bayan sulhun Amurka da Iran.

Source: Getty Images
An kai sojan Isra'ila asibiti
Rahoton Times of Israel ya tabbatar da hadarin da ya rutsa da sojan Isra'ila a Lebanon, inda ya ce har yanzu rundunar kasar na ci gaba da binciken musabbabin fashewar da ta jikkata sojan.
Bisa binciken farko na IDF ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana, yayin wani samame da Rundunar Commando Brigade ke gudanarwa a ƙauyen Arnoun.
"An garzaya da sojan zuwa asibiti domin samun kulawa, kuma an sanar da iyalansa,"
In ji rundunar.
Isra'ila kai hari kasar Lebanon
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Lebanon sun ruwaito a ranar Litinin cewa an kai hari ta sama a Kudancin ƙasar, duk da yarjejeniyar da Lebanon da Isra'ila suka sanya wa hannu a makon da ya gabata domin samar da zaman lafiya.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Lebanon ya ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a yankin da ke tsakanin garuruwan Qantara da Deir Seryan da ke Kudancin ƙasar.
Amurka ta gana da Isra'ila
Kwamandan rundunar Amurka (CENTCOM), Brad Cooper, ya gana da manyan jami'an gwamnati da na soja a Isra'ila da Lebanon yayin wata ziyara da yake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.
A Lebanon, Roya News ta rahoto Cooper ya tattauna da shugaban kasar Joseph Aoun da kwamandan sojojin Lebanon, Rodolphe Haykal.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan aiwatar da wata yarjejeniyar da aka sanya wa hannu kwanan nan a Washington DC domin tsara sababbin matakan tsaro.

Source: Getty Images
Ziyarar na zuwa ne yayin da Amurka ke ci gaba da hulɗa da shugabannin sojojin Lebanon a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikicen yankin da kuma ƙoƙarin ƙarfafa cibiyoyin gwamnati.
A Isra'ila kuwa, Cooper ya ziyarci sojojin Amurka da ke bakin aiki tare da karrama wasu daga cikinsu bisa abin da CENTCOM ta bayyana a matsayin gagarumar gudunmawa da suka bayar wajen gudanar da ayyuka.
Jirgin Isra'ila ya samu matsala
A wani labarin, mun kawo muku cewa jirgin da ke dauke da shugaban kasar Isra'ila ya samu matsala yayin da ya ke tafiya a sararin samaniya.
Bayan tasowa daga wajen ta'aziyya, jirgin shugaban kasar ya yi karo da wani garken tsuntsaye, lamarin da ya tilasta masa saukar gaggawa.
Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa ta sauya wa shugaban kasar jirgi kuma za ta kaddamar da bincike domin gano dalilin faruwar lamarin.
Asali: Legit.ng

