"Baka Isa ba," Jigon ADC Ya Takawa Wike Birki kan Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Cif Eze Chukwuemeka Eze ya maida martani ga Ministan Abuja, Nyesom Wike kan kalaman da ya yi cewa Atiku ba zai taba zama shugaban kasa ba
- Jigon na ADC ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa Wike ya yi ikirarin yana da tsarin siyasa da zai tabbatar da cewa Atiku ya sake shan kaye a 2027
- Eze ya jaddada cewa babu wani dan siyasa, komai mukaminsa ko tasirinsa, da zai iya yanke hukuncin wanda zai zama shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Wani jigo a jam’iyyar ADC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi watsi da kalaman da ake dangantawa da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.
Tun farko Wike ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ba zai taba zama shugaban Najeriya ba.

Source: Facebook
Leadership ta ce a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Fatakwal ranar Litinin, Eze ya ce babu wani mutum da ke da ikon tantance wanda zai zama shugaban Najeriya a zaben 2027.
Eze ya caccaki Wike kan zaben 2027
Eze ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa Wike ya yi ikirarin yana da tsarin siyasa da zai tabbatar da cewa Atiku ya sake shan kaye a zaben shugaban kasa na 2027.
Ya bayyana irin wannan ikirari a matsayin abin takaici, rashin mutunta dimokuradiyya da kuma nuna girman kai, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa, irin wadannan kalamai na nuna wata fahimta mai hatsari da ke kokarin daukaka mutum guda sama da zabin al'ummar Najeriya.
Jigon ADC ya nemi karin haske daga Wike
Jigon na ADC ya kalubalanci Ministan Abuja da ya bayyana irin "tsarin siyasa" da yake yawan ambata a jawabansa.
Eze ya ce 'yan Najeriya na da hakkin sanin ko Wike na magana ne kan tsarin da ya ginu bisa amincewar jama'a da kuri'unsu, ko kuma wani da ake zargin ya dogara da amfani da karfin iko, tsoratar da 'yan adawa da kuma amfani da hukumomin tsaro.
Ya ce:
"Yana da muhimmanci Wike ya bayyana wa 'yan Najeriya abin da yake nufi da tsarin siyasa. Tsarin jama'a ne ko tsarin iko?
"Shin tsarin ya ginu ne bisa ka'idojin dimokuradiyya ko kuma tsarin da aka gina kan tsoratar da 'yan adawa da magudi? Wadannan tambayoyi ne da 'yan Najeriya suka cancanci amsarsu."

Source: Facebook
Eze ya jaddada cewa babu wani dan siyasa, komai mukaminsa ko tasirinsa, da zai iya yanke hukuncin wanda zai zama shugaban kasa.
Atiku ya yi zargin ana shirin rusa ADC
A wani rahoton, kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa a ADC, Alhaji Atiku Abubakar ya yi zargin cewa ana ana kulla wani shiri da zai hana jam'iyyarsa shiga zaben 2027.
Atiku ya ce ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana haɗa kai ta fannin siyasa da shari'a domin hana ADC bayyana a takardar kaɗa ƙuri'a a zaɓen 2027.
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya, ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ba, da su yi tir da duk wani yunƙuri na bai wa jam'iyya mai mulki damar zaɓar waɗanne jam'iyyun adawa za su shiga takara.
Asali: Legit.ng

